Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

  • Peter Obi mai neman shugabancin Najeriya a LP ya jawo abin magana saboda ya ziyarci babban malamin musulunci, Dr. Ahmad Abubakar Gumi
  • Legit.ng Hausa ta fahimci tun da aka ga Ahmad Abubakar Gumi tare da Obi, magoya bayan ‘dan takaran suke tofa albarkacin bakinsu game da batun
  • Wasu sun yabi tsohon gwamnan na jihar Anambra da yin zama da wanda yake da alaka da ‘yan ta’adda, wasu suna ganin wannan siyasa ta gada

Kaduna - A cikin magoya bayan Peter Obi, akwai wadanda sun kausasa harshe a kan Ahmad Gumi a baya, saboda kokarinsa na kawo zaman lafiya a Arewa.

Ziyarar da gwaninsu ya kai zuwa gidan shehin malamin a Kaduna ya jawo wasu sun lashe amansu.

Premium Times tace a yayin da wasu suke cewa sun fasa ba ‘dan takaran kuri’arsu, wasu sun fito sun wanke shi daga zargi, sun nemawa gwaninsu uzuri.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Na Tambayi Peter Obi a Zaman da Nayi da Shi inji Sheikh Ahmad Gumi

Peter Obi
Peter Obi a Arewa House Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin mutane a Twitter

“Tambaya har cikin zuciya ta Peter, kana jin dadin yadda siyasa ta maida ka haka? Domin kuwa na fasa zaben ka a yanzu.”

- Ogwuefe Bunkoye

“Peter Obi, ina fatan wannan katangar da ke ginawa ba za ta hade da Buhari a wani lokaci nan gaba ba, domin na daina fahimtarka.”

- Fakoyejo Olalekan

@Morris_Monye ya rubuta:

“Wannan shi ake kira hada alaka. Gumi dai ‘dan Najeriya ne. Babu kotun da ta kama shi da laifi. Za a shiga har inda APC tayi karfi da wuraren da suke da wahalar shiga.”

Wani kuma yake cewa:

Wannan tafiya ta #Obidient ta hadin-kai ce, babu wariya, babu abokin gaba na din-din-din, sai dai kishin kasa na din-din-din.

The Cable ta rahoto Daniel Regha yana kaca-kaca da masu kokarin kare Peter Obi, yace babu dalilin haduwa da wanda yake ba ‘yan bindiga kariya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Arewa na Shirin Goyon Bayan Wani ‘Dan Takara ‘Mara Shahara’

Wata mai suna NK£M #PeterObi2023 tana mai kokawa tace:

Peter Obi, kowa ya san kabilancin Sheikh Gumi, ba ko ina za a rika shiga ba.

Shi ma @Dynast598084681 yace Sheikh Gumi yana sulhu da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, don haka babu dalilin da Obi zai kai masa ziyara.

Vanguard ta rahoto wani @Godnogowyneyou yana cewa ‘dan takaran ya yi dabara da ya zauna da Gumi domin malamin yana da tasiri fiye da kima.

Abin da na tambayi Obi - Gumi

Kamar yadda ya yi bayani, kun ji labari Dr. Ahmad Gumi ya tasa 'dan takaran na zaben 2023 da tambayoyi domin ya san manufofinsa da irin akidunsa.

Jerin tambayoyin da Malamin fikihun ya yi wa Peter Obi sun shafi fasalin shugabanci da tsarin kasa, zaman lafiya da yadda zai kawo ayyukan yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel