Abubuwan da Na Tambayi Peter Obi a Zaman da Nayi da Shi inji Sheikh Ahmad Gumi

Abubuwan da Na Tambayi Peter Obi a Zaman da Nayi da Shi inji Sheikh Ahmad Gumi

  • Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya zauna da Peter Obi mai neman kujerar shugaban kasa a 2023
  • Malamin addinin ya yi wa ‘dan takaran wasu tambayoyi domin ya ji ra’ayoyi da irin manufofinsa
  • Shehin ya nemi jin ta-bakin ‘Dan takaran LP a kan fasalin kasa da yadda zai samar da ayyukan yi

Kaduna - Babban malamin addinin Musulunci, Ahmad Abubakar Gumi ya yi bayanin tattaunawarsa da Mista Peter Obi a lokacin da ya kai maso ziyara.

Peter Obi mai neman zama shugaban kasar Najeriya a zaben 2013 ya zo gidan Sheikh Ahmad Abubakar Gumi. Daily Trust ta rahoto irin wainar da aka toya.

A cewar shehin malamin, ya yi wa ‘dan takaran wasu tambayoyi domin ya ji inda ya sa gaba.

Kara karanta wannan

Ba Mu da Wani 'Dan takara a Ran Mu - Kwamitin Arewa Ya Fadawa Kwankwaso

Sheikh Ahmad Gumi ya shaidawa jaridar a wata hira ta musamman cewa ya gana da ‘dan takaran ne a hanyarsa ta zuwa taro da kwamitin hadakan Arewa.

An rahoto Ahmad Abubakar Gumi yana mai cewa Peter Obi bai iya bada cikakkun amsoshi a nan-take ba saboda lokaci da yanayin da ya samu kan shi.

Sheikh Ahmad Gumi
Peter Obi da Ahmad Gumi a Kaduna Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shi (Obi) ya kawo mani ziyara duk da wannan ne karon farko da na hadu da shi ido-da-ido, na gode da ziyarar da ya kawo.
Nayi masa muhimman tambayoyi, kuma na fada masa bai ba ni amsoshi kai-tsaye ba.
Tun da yana hanyar zuwa Arewa House ne, a nan za iyi wa dinbin jama’a bayani da kyau domin su fahimta."

- Dr. Ahmad Abubakar Gumi

Tambayoyin da aka yi wa Peter Obi

"Na tambaye shi a game da matsayarsa a kan sauya fasalin kasa domin tun 1960 har zuwa yau, ana ta canza tsarin kasar nan

Kara karanta wannan

Manta da Elon Musk, Ga Labarin Mansa Musa, Basaraken Afrika da ya Ninka Musk Arziki

Na kuma tambaye shi a game da yadda zai inganta rayuwar mutane marasa kwarewar aiki."

- Dr. Ahmad Abubakar Gumi

A hirar da aka yi da shi, malamin addinin ya nemi jin ta bakin ‘dan takaran kan batun kasashen waje, sannan ya ba shi shawara kan takaran da yake yi.

"Sannan nayi masa tambaya a kan yadda zai lallashi mutanen Kudu maso gabas, Arewa maso tsakiya, kudu maso yamma da kuma Arewa maso gabas.
Na fada masa kasashen ketare suna cikin masu raban kan mu a siyasa domin jin yadda zai bullowa lamarin, kuma ya yarda da ni, nayi masa fatan alheri."

- Dr. Ahmad Abubakar Gumi

Rikicin gidan PDP

Kuna da labari Gwamnan jihar Ribas da ake ta rikici da shi a PDP, NyesomWike yace zai mara baya ga tikitin Atiku/Okowa a zaben Shugaban kasa na 2023.

Nyesom Wike yace tun da ya sallamawa ‘dan takaran jam’iyyar adawar, dole a maye gurbin Iyoricha Ayu da wani ‘Dan Kudu, domin ayi wa yankinsa adalci.

Kara karanta wannan

Sunan Darektan Kamfe a APC Ya Fito a Kwamitin Yakin Neman Zaben Peter Obi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel