Zan Gina Sabuwar Jami'ar Kiristoci A Jihar Neja, TY Danjuma

Zan Gina Sabuwar Jami'ar Kiristoci A Jihar Neja, TY Danjuma

Tsohon Ministan Tsaro, Janar Theophilus Danjuma, ya bayyana cewa zai gina sabuwar jami'ar Cocin Anglican na farko a Arewacin Najeriya.

Danjuma yace zai yi wannan gini ne a garin Dikko, jihar Neja kuma za'a sanyawa wannan jami'a suna Walter Miller.

A jawabin da ya gabatar ranar Laraba a Legas yayin liyafar dare, TY Danjuma ya bayyana cewa shekaru biyu da suka gabata suka fara shawaran gina jami'ar bayan ganawarsa da wasu Bishap-Bishap.

Yace tuni an kaddamar da shiri sosai wajen fara ginin.

TY Danjuma
Zan Gina Sabuwar Jami'ar Kiristoci A Jihar Neja, TY Danjuma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace:

"Shekaru biyu da suka gabata wasu jajirtattun Malamai da Bishap karkashin jagorancin Farfesa Adamu Baikie suka sameni kuma suka mun bayanin bukatar ginin jami'ar."

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Kashe Saurayinta Da Wuka Cikin Dare Kusa Da Dakin Hotel

"Yanzu dai an samu nasara sosai wajen kafa jami'ar kuma muna neman gudunmuwarku."

Gwamnan jihar Neja, Abubuakar Sani Bello, wanda ya halarci taron ya jinjinawa TY Danjuma bisa wannan aiki.

Ya baiwa jami'ar filin Hekta 100 kyauta don ginin.

Yace:

"Babu mutum irinka da yawa a Najeriya yau. Muna alfahari da kai. Kai Ubanmu ne kuma kayi naka."

Asali: Legit.ng

Online view pixel