Da Duminsa: Atiku Ya Shilla Turai Ana Tsaka da Gangamin Yakin Neman Zabe

Da Duminsa: Atiku Ya Shilla Turai Ana Tsaka da Gangamin Yakin Neman Zabe

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP yayi tafiya zuwa Turai a daren Litinin da ya gabata
  • Rohotanni sun bayyana yadda Atiku ya yi tafiyar don neman lafiyarsa, duk da dai kakakinsa, Paul Ibe ya musanta hakan
  • Atiku da Asiwaju Bola Tinubu sun samu damar ganawa a Turai duk da kasancewarsu manyan abokan adawa a zaben shekara mai zuwa

‘Dan Takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi tafiya zuwa kasar Turai.

Atiku Abubakar
Da Duminsa: Atiku Ya Shilla Turai Ana Tsaka da Gangamin Yakin Neman Zabe
Asali: Depositphotos

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bar kasar ne bayan ya gana da Asiwaju Bola Tinubu, ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar APC, a filin sauka da tashin jiragen Nnamdi Azikiwe dake Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

An samu rahotannin dake bayyana yadda ‘dan takarar jam’iyyar PDP ya bar kasar don neman lafiyarsa, amma sai dai Paul Ibe, mai magana da yawunsa, ya musanta hakan, tare da cewa Atiku ya yi tafiyar ne don kasuwanci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Tsohon mataimakin shugaban kasan ya fita kasar waje a daren jiya tare da abokan kasuwancinsa na daya daga cikin kasuwancinsa da ta samu tangarda saboda kullen Oktoba da rushewar tattalin arziki.”
“Taron zai maida hankali ne wajen neman mafita akan yadda za’a bunkasa kayayyakin da kasuwancin da ake samarwa,” a cewar Ibe a wata takarda.

Kakakin bai bayyana takamaiman kasar da Atiku ya je ba.

‘Dan takarar yayi watsi da kamfen dinsa a jihar Akwa Ibom a makon da ya gabata, gami da garzayawa zuwa Kaduna a ranar Litinin.

‘Yan daba sun kaiwa magoya bayansa hari a wajen zagaye, wanda yayi matukar bata masa rai, hakan yasa yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi jan kunne ga sauran jam’iyyu da magoya bayansu da su tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba

Yayin da Atiku ya aje kamfen dinsa, daya daga cikin manyan abokan adawarsa na zaben shekara mai zuwa Tinubu na Turai.

PDP sun amfani da hakan a matsayin abun magana, inda suke cewa rashin ‘dan takarar jam’iyya mai mulkin a kasar na nuna bai shirya jagorancin ba.

2023: Atiku Ya Bayyana Manufofi 5 Da Zai Yi Amfani Da Su Don Tsallakar Da Najeriya Zuwa Ga Tudun Mun Tsira

A wani labari na daban, a ranar Laraba, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa ya saki burikansa biyar wadanda ya ke son cikawa da zarar an zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Ya saki kudirorin nasa guda biyar ne ta shafinsa na Twitter yayin da ake shirye-shiryen zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP a karshen makon nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel