Atiku: Yan Arewa Na Bukatar Dan Arewa Ya Zama Shugaban Kasa Ba Bayarabe Ko Inyamuri Ba

Atiku: Yan Arewa Na Bukatar Dan Arewa Ya Zama Shugaban Kasa Ba Bayarabe Ko Inyamuri Ba

  • Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya kada gangar kabilanci gabannin babban zaben 2023
  • Atiku Abubakar ya fadama taron yan arewacin kasar cewa basa bukatar shugaban kasa dan kabilar Yarbawa ko Inyamuri
  • Da yake jawabi a wani taro da ya gudana a Zaria, Atiku yace abun da suke bukata a yanzu shine wani dan arewa ya sake karbar mulki daga hannun shugaba Buhari

Kaduna – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yan arewa na bukatar wani shugaban kasa da ya fito daga yankin arewacin kasar.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, a wani taron yan arewa da aka gudanar a jihar Kaduna, The Cable ta rahoto.

Atiku Abubakar
Atiku: Yan Arewa Na Bukatar Dan Arewa Ya Zama Shugaban Kasa Ba Bayarabe Ko Inyamuri Ba Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Yayin da yake jawabi ga taron al’ummar Hausa Fulani da dama, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa basa bukatar dan Igbo ko bayarabe a matsayin shugaban kasa sai dai wani daga arewa.

Ya bayyana cewa ya ketara jihohi 36 a Najeriya kuma ya fahimci banbance-banbancen su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku ya ce ya kamata yan arewa su yarda dashi ta hanyar basa kuri’unsu, yana mai cewa shine yafi cancanta da zama shugaban kasa.

Vanguard ta nakalto yana cewa:

“Na kutsa koina a fadin kasar nan.
“Na san gaba daya kasar nan. Na gina gada a fadin kasar. Ina ganin abun da dan arewa ke bukata shine wani da ya fito daga arewa, kuma wanda ya fahimci sauran yankunan Najeriya kuma wanda ya gina gada a fadin sauran yankunan kasar.
“Wannan shine abun da dan arewa ke bukata. Shi (dan arewa) baya bukatar dan takara Bayarabe, ko dan takara inyamuri. Wannan shine abun da dan arewa yake bukata.
“Na tsaya gabanku a matsayin dan Najeriya mai kishin kasa daga tsatson arewa.”

Atiku Ne Ya Bani Shawaran In Karbi N1bn Amma Na Ki, Iyorchia Ayu

A wani labarin, shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party, Senator Iyorchia Ayu, ya bayyana cewa dan takarasu Atiku Abubakar ya bashi shawarar karban bashin N1bn amma ya ki.

Ya bayyana hakan ne yayin martani ga Wike wanda ya zargesa da karban N1bn daga wajen wani gwamna.

Ayu ya bayyana cewa tun lokacin da ya hau kujerar ya tarar jam'iyyar bata da kudi amma duk da haka bai karbi ko sisi hannun wani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel