Ban Sani Ba Ko Tinubu Yana Najeriya, Inji Jigon Kamfen Din Tinubu, Oshiomole

Ban Sani Ba Ko Tinubu Yana Najeriya, Inji Jigon Kamfen Din Tinubu, Oshiomole

  • Tsohon gwamna kuma minista Adams Oshiomole ya yi wata magana mai daukar hankali game dan takarar shugaban kasa na APC
  • A cewarsa, bashi da masaniyar inda Bola Ahmad Tinubu yake a yanzu, don haka ba zai iya cewa komai game dashi ba
  • An fara gangamin kamfen din 2023 a Najeriya, 'yan siyasa sun fara tallata hajojinsu na gaje kujerar Buhari

Najeriya - Mataimakin daraktan gangamin kamfen din APC, Adams Oshiomole ya ce bai da masaniya ko dan takarar shugaban kasansu na nan a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 28 ga watan Satumba yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels.

Adams Oshiomole ya ce bai san inda Tinubu yake ba a yanzu
Ban Sani Ba Ko Tinubu Yana Najeriya, Inji Jigin Kamfen Din Tinubu, Oshiomole | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa:

"Ba da shi nake aiki kullum ba, ban san yana nan ko bai nan ba."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Kamfen zaben 2023: Tinubu ya fadi sassan da zai tafi yawon kamfen a Najeriya

Oshiomole, wanda shine tsohon shugaban APC ya ce har yanzu ba a kaddamar da majalisar kamfen din takarar shugaban kasa na jam'iyyar ba.

Buhari ne shugaban kamfen

Shugaba Buhari ne shugaban tawagar kamfen din da aka fara a Najeriya.

An ce Tinubu ya shilla kasar Burtaniya yayin da ake shirin fara gangamin, duk da cewa ba a tabbatar da tafiyar tasa ba a hukumance, inji Channels Tv.

A ranar ta Laraba ne dai, Tinubu ya saki wata sanarwa da ke bayyana kadan daga abubuwan da ya tsara a gangamin da aka fara.

An sha cece-kuce kan yadda lafiyar Bola Tinubu ke kasancewa, ganin shekaru sun ja gashi yana yawan kwanciya rashin lafiya.

Ga kuma yadda zabe ke kara gabatowa, jam'iyyar APC bata kammala shiri mai karfi ba.

Zan Yi Kamfen A ‘Kowane Sashe Na Najeriya’, inji Dan Takarar APC Tinubu

A wani labarin na daban kuma, kun ji rahoton da muka kawo na cewa, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga shirinsa na kamfen din zaben 2023, Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Hotuna Sun Bayyana A Yayin Da Peter Obi Ya Kaddamar Da Kamfen Dinsa A Babban Jihar Arewa

Tinubu ya ci alwashin cewa, zai taka kowane bangare a Najeriya domin tallata aniyarsa ta gaje kujerar Buhari a 2023.

A baya an yada jita-jitar cewa, akwai yiwuwar lafiyar Tinubu ta hana shi samun damar yawo a jihohin Najeriya da sunan kamfen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel