Kwararan Majiyoyi Sun Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa APC Ta Dakatar Da Fara Kamfen Har Sai Baba Ta Gani

Kwararan Majiyoyi Sun Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa APC Ta Dakatar Da Fara Kamfen Har Sai Baba Ta Gani

  • An zargi, Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ta nada direktoci da mataimakansu ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba
  • An rahoto cewa wasu gwamnonin arewa ba su ji dadin nadin Falake da Adams Oshiomhole a kwamitin kamfen ba, ana zargi kudu suke yi wa aiki
  • Ana zargin Falake, sakataren kwamitin kamfen din na APC da yin mulki tamkar a kungiyar masu aikata manyan laifuka, hakan ma ya kara kan dalilan dakatar da kamfen din

FCT Abuja - Kwararran majiyoyi a jam'iyyar APC sun bayyana cewa dakatar da fara kamfen din jam'iyyar ba zai rasa alaka da yadda Tinubu ke gudanar da harkokin kwamitin takarar shugaban kasar ba, This Day ta rahoto.

Shugaban kungiyar kamfen din takarar shugaban kasar na APC, (PCC), kuma gwamnan Jihar Plateau, Simon Lalong, ya sanar da dage fara kamfen din a ranar Talata da aka shirya kaddamarwa ranar Laraba 28 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

An Gano Yadda Tinubu Ya Assasa Rikicin APC kan Kwamitin Yakin Neman Zabensa

Bola Ahmed Tinubu
Kwakwarar Majiya Ta Bayyana Dalilin Da Yasa APC Ta Dakatar Da Fara Kamfen Har Sai Baba Ta Gani. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi Tinubu da zaben direktoci da mataimakan direktocin kamfen ba tare da tuntuba ba

Mambobin jam'iyya da dama suna zargin Tinubu da nada wasu mutane a matsayin direktoci ko mataimakan direktoci a kwamitin ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.

Wasu da dama suna ganin hakan tamkar kamar wani yunkuri ne na kwace sakatariyar kamfen din, musamman bayan nadin James Falake, dan majalisar Legas a matsayin sakataren kamfen.

Majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin sun bayyana cewa arewa maso tsakiya ya kamata a bawa kujerar sakatare a wani mataki na kwantar musu da hankali ganin sune marasa rinjaye a arewa.

Amma, saboda direkta na PCC, Gwamna Simon Lalong, ya fito ne daga Jihar Plateau, an amince a bawa jihar Benue, kujerar sakatare, kasancewarta jiha mai muhimmanci a yankin tsakiya.

Kara karanta wannan

Babu Banbanci Tsakanin Obi, Atiku Da Tinubu, In Ji Kachikwu, Dan Takarar Shugaban Kasa Na ADC

Yadda Tinubu ya ki amincewa da bukatar yankin tsakiya su zabi sakataren PCC

Bayan hakan, an rahoto cewa wani gwamnan jihar arewa ta tsakiya ya tuntubi tsohon gwamnan jihar Benue, George Akume, ya aika sunan mutane biyu da takardunsu don Tinubu ya duba yiwuwar basu mukami, kuma ya tura.

Amma tsohon gwamnan jihar na Legas wai bai amince da sunayen daga jihar Benue ba.

Daga Karshe, Shettima Ya Magantu Kan Salon Shigar Da Ya Yi Zuwa Taron NBA

A wani rahoton, Sanata Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya magantu kan cece-kuce da aka rika yi kan salon shigar da ya yi zuwa taron NBA a ranar Litinin.

Shettima, wanda ya wakilci Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ya dauki hankulan mutane a dandalin sada zumunta bayan daya cikin hotunansa a taron ya bazu.

Kara karanta wannan

Chimaroke Nnamani: Sanatan PDP Da Aka Sunansa A Kwamitin Kamfen Din Tinubu Ya Yi Martani, Ya Faɗa Jam'iyyar Da Zai Yi Wa Kamfen

Asali: Legit.ng

Online view pixel