Takaitaccen tarihin Dogarin Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha

Takaitaccen tarihin Dogarin Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha

Manjo Hamza Al-Mustapha shararren Soja ne wanda ya zama Dogarin tsohon shugaban Najeriya, Janar Sani Abacha. A wannan lokaci ne sunansa ya ratsa ko ina a kasar nan.

Legin.ng Hausa ta tsakuro maku kadan daga cikin tarihin Hamza Al-Mustapha:

1. Haihuwa da tashi

An haifi Hamza Al-Mustapha ne a Garin Nguru, jihar Yobe kafin Najeriya ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960. Al-Mustapha ya shiga gidan soja ne a boye, ya samu hora a makarantar sojoji ta NDA da ke garin Kaduna.

2. Gidan Soja

Al-Mustapha soja ne mai matukar basira da kaifin tunani. Rahotanni sun bayyana cewa Manjo Hamza Al-Mustapha ya na da hannu wajen binciken wasu juyin mulki biyu da aka yi.

3. Dogarin Abacha

Bayan kifar da gwamnatin sojan Muhammadu Buhari ne Sani Abacha ya zama shugaban sojin kasa. A wannan lokaci Al-Mustapha ya zama ADC ga Janar Sani Abacha na shekaru biyar.

Daga baya ya zama babban jami’in tsaro watau CSO na Sani Abacha bayan sun kifar da gwamnati. Abacha ya ba Al-Mustapha karfi inda ya ke da ikon yin abin da ko manyan ba za su yi gigi ba.

A lokacin mulkin Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha da wasu manyan jami’ai sun ci karensu babu babbaka, su ka kuma rika horas da Dakaru a kasashe irinsu Israila da Koriya ta Arewa.

KU KARANTA: Mai dakin Mataimakin Janar Sani Abacha ta rasu

4. Mutuwar Abacha

Manjo Hamza Al-Mustapha ya na cikin wadanda su ka fara samun labarin mutuwar Sani Abacha da abubuwan da su ka faru a wannan lokaci. Jim kadan bayan mutuwar Abacha, aka tsare shi.

5. Gidan yari

Bayan ‘dan lokaci aka fara binciken Hamza Al-Mustapha da zargin juyin mulki da kisan kai, wannan ya kai shi gidan yari har ya shafe shekaru 15.

A 2012 kotu ta same shi da laifin kashe Kudirat Abiola, aka yanke masa hukuncin kisa. Kotun daukaka kara ta yi watsi da wannan hukunci a 2013.

6. Samun ‘yanci

Al-Mustapha ya shafe shekaru 15 ya na tsare a kurkuku, a tsawon wannan lokaci Alkalai kusan 15 su ka yi aiki a kan shari’arsa. Bayan fitowarsa daga gidan yari, ya koma Garin Kano da zama.

7. Siyasa

A 2017 Al-Mustapha ya shiga siyasa, ya kafa jam’iyyar GPN wanda ta ke tafiya da matasa. A zaben 2019, jam’iyyar PPN ta tsaida tsohon sojan a matsayin ‘dan takarar shugaban kasar ta a zaben da APC ta lashe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel