Sanatan PDP Da Aka Sunansa A Kwamitin Kamfen Din Tinubu Ya Yi Martani, Ya Faɗa Jam'iyyar Da Zai Yi Wa Kamfen

Sanatan PDP Da Aka Sunansa A Kwamitin Kamfen Din Tinubu Ya Yi Martani, Ya Faɗa Jam'iyyar Da Zai Yi Wa Kamfen

  • Chimaroke Nnamani, sanatan jam'iyyar PDP daga jihar Enugu, ya ce Tinubu abokinsa ne, dan uwa kuma takwara da ya ke girmamawa amma jam'iyyarsa zai yi wa kamfen
  • Tsohon gwamnan na jihar Enugu ya furta hakan ne a matsayin martani kan tambayar da aka masa na cewa ko zai goyi bayan dan takarar shugaban kasar na APC
  • Yan Najeriya sun yi mamakin lokacin da suka ga sunan Nnamani a jerin wadanda Tinubu ya saka a kwamitin kamfen dinsa

Twitter - Chimaroke Nnamani, sanatan jam'iyyar PDP daga jihar Enugu, ya ce Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC "abokinsa ne, dan uwa kuma takwara."

Sanata Nnamani ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 27 ga watan Satumba, yayin da ya ke amsa tambaya da wani mai amfani da Twitter, Henry Shield (@henryshield) ya masa na neman sanin ko Tinubu ya ke yi wa aiki.

Kara karanta wannan

"Ba Kuskure Bane" Jam'iyyar APC Ta Faɗi Dalilin Sanya Jigon PDP a Kamfen Tinubu, Ta Maida Martani Ga Gwamnoni

Tinubu da Nnamani
Chimaroke Nnamani: Sanatan PDP Da Aka Sunansa A Kwamitin Kamfen Din Tinubu Ya Yi Martani. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Senator Chimaroke Nnamani.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan za a iya tunawa sunan Nnamani, sanatan PDP mai wakiltan Enugu East, na cikin sunayen mutane 422 na kwamitin kamfen din APC.

Shield ya yi tambaya a Twitter:

"Yanzu da ni da tsohon Gwamna @ChimarokeNamani na bin juna kuma duba da tambayar da Festus Keyamo ya bada na saka sunan tsohon gwamnan a kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC kwanaki da suka shude a Channels, zan sake tambaya, Mai girma, shin kana yi wa Tinubu aiki?"

A martaninsa, Nnamani ya ce shi dan PDP ne mai biyayya ga jam'iyya kuma jam'iyyarsa zai yi wa kamfen.

Tsohon gwamnan ya ce yana matukar girmama Tinubu, a yayin da ya wallafa bidiyonsa yana nuna kin amincewarsa da kudirin dokar soshiyal midiya a zauren majalisa.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023

Ya rubuta:

"Ya kai Henry Nwazuruahu. Nagode da ka bi ni da girmama bin wanda ya bi ka. Demokradiyya abu ne mai ban sha'awa. Ni dan PDP ne, Sanatan PDP. Mai biyayya ga jam'iyya kuma jam'iyya na zan yi wa kamfen.
"Shi Tinubu abokina ne, dan uwa kuma takwara. Ina girmama shi sosai, siyasarsa da nasarorin da ya samu a gwamnati. Kuma na gamsu da shi. Duk wanda cikinsu ke masa ciwo ya tafi .... kansa."

Tikitin Musulmi Da Musulmi: Jerin Mukaman Da Kiristocin Najeriya Za Su Iya Samu A Gwamnatin Tinubu

Bayan sukar da aka rika yi kan tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar APC ta yi, Kungiyar matasa kirista na 'Christian Youths Movement for Tinubu/Shettima' ta bayyana cewa akwai mukamai kiristoci za su iya samu idan Tinubu ya ci zaben 2023.

Idan za a iya tunawa zaben tsohon gwamnan na Jihar Borno, Kashim Shettim a matsayin abokin takarar Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023 ya janyo cece-kuce a kasar.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Wa Wike Tayin Kujerar Sanata? Gwamnan Na Rivers Ya Fayyace Gaskiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel