Masoya Sun Rude da Jin Rade-radin Kai wa ‘Dan takarar Shugaban Kasa Hari

Masoya Sun Rude da Jin Rade-radin Kai wa ‘Dan takarar Shugaban Kasa Hari

  • A farkon makon nan jita-jita ta fara yawo, ana cewa wasu sun kai wa Peter Obi hari a garin Abuja
  • Hadimin ‘dan takaran shugaban kasar, Valentine Obienyem yace babu kanshin gaskiya a labarin
  • Valentine Obienyem yace Peter Obi yana nan lafiya kalau tun da ya dawo Najeriya daga kasashen waje

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Mai magana da yawun bakin Peter Obi, Valentine Obienyem ya musanya labarin da ake ji na kai ‘dan takaran shugaban kasar hari.

Tribune ta rahoto Kwamred Valentine Obienyem yana cewa jita-jitar da ta karada gari a kan harin da aka kai wa mai gidansa, ba gaskiya ba ne.

A ranar Litinin, 12 ga watan Satumba 2022, wasu suka fara yawo da labarai cewa an kai wa ‘dan takaran LP a 2023 hari a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

APC Ta Yi Magana Kan Lafiyar Bola Tinubu da Yiwuwar Janye Takarar Shugaban Kasa

Hadimin ‘dan takaran shugaban kasar yake cewa Peter Obi yana nan garau cikin koshin lafiya tun bayan dawowarsa gida daga kasashen waje.

Obi ba ya tada rikici a siyasa

Jawabin Obienyem yace uban gidansa bai yarda da gabar siyasa ba don haka bai goyon bayan a rika tada zaune tsaye da sunan neman mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“’Dan takaran jam’iyyar Labour Party kuma shugaban kasar gobe da yardar Ubangiji, Peter Obi ya dawo kasar nan.
Peter Obi
Peter Obi ya yi tagumi Hoto: Peter Obi Grassroots Mobilization
Asali: Twitter

Makonni uku da suka wuce yana yawo a kasashen Duniya, yana kira ga ‘yan Najeriya da su karbe kasar da suka mallaka.”
“Kuyi watsi da rade-radin da ke yawo a gari na kai masa hari. Ubangiji ya tsare wannan mugun aiki daga faruwa a kan shi
“Obi ya dade yana nanata akidarsa na yin siyasa ba tare da tada rigima ba. Wannan shi ne tafarkin da ya yi imani da shi.”

Kara karanta wannan

2023: Ana Gabanin Fara Kamfe, Kwankwaso Ya Ja-kunnen Tinubu, Atiku da Peter Obi

- Valentine Obienyem

Martani ga Festus Keyamo

“Labarin da ke zuwa bayan jawabin da Festus Keyamo ya fitar, yana ikirarin Obi zai yi karyar an kai masa hari, abin takaici ne.”
“Wannan ya nuna babu mamaki shedanu suna kitsa wannan danyen aiki.”

- Valentine Obienyem

A karshe, an rahoto Obienyem yace za su cigaba da addu’a ga Ubangiji ya kare ‘dan takaran.

Legit.ng ta fahimci tuni mutane suka fara surutu a shafuka da dandalin sada zumunta, suna cewa wajibi ne a kare lafiyar 'dan takaran.

Yadda za a ci zabe - Kungiya

Kuna da labari wata kungiya ta masoyan Peter Obi mai suna Peter Obi Support Group tana harin jihohi biyar da za su Labor Party ta ci zabe a 2023.

Shugaban POPSG a Duniya, Felix Obaze yace jihohin da suke kwallafa rai a kai sun hada da Legas, Ribas Kano, da Kaduna, sai kuma garin Abuja.

Kara karanta wannan

Allah-wadai: Rikici ya barke tsakanin Mali da Cote D'Ivoire, Buhari ya sha alwashin warwarewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel