2023: Abin Da Na Fada Wa Matar Tinubu Lokacin Da Ta Bukaci In Goyi Bayan Mijinta, Dele Momodu

2023: Abin Da Na Fada Wa Matar Tinubu Lokacin Da Ta Bukaci In Goyi Bayan Mijinta, Dele Momodu

  • Mawallafin mujjalar Ovation, Cif Dele Momodu ya magantu kan abin da ya faru tsakaninsa da Oluremi Tinubu, matar Asiwaju Bola Tinubu
  • Tsohon mai neman takarar shugaban kasar na PDP ya ce matar Tinubu ta masa tambaya kan dalilin da yasa ba zai yi wa mijinta kamfen ba
  • Momodu ya ce bayan ya yi murmushi, ya bude baki ya fada mata cewa shi dan PDP ne don haka ba zai iya yiwa dan wata jam'iyyar daban kamfen ba

Jihar Legas - Dele Momodu, mawallafi kuma dan siyasa, ya bayyana abin da ya faru tsakaninsa da Sanata Oluremi Tinubu, matar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC.

Momodu na daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a PDP, a zaben da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe.

Kara karanta wannan

2023: Ainihin Sababin Rikicin Wike Da Atiku, Jigon Jam'iyyar PDP Ya Yi Bayani

Dele Momodu
2023: Abin Da Ya Faru Tsakani Na Da Matar Tinubu, Dele Momodu. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

A ranar Alhamis, Momodu da matar Tinubu sun hadu wurin jana'izar Kemi Nelson, jigo na jam'iyyar APC a Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke bada labarin abin da ya faru yayin haduwarsa da sanatan a shafinsa na Instagram, Momodu ya rubuta:

"Mutum biyu kacal, bayan masu daukan hoto suka ga abin da ya faru tsakanina da Sanata Oluremi Tinubu jiya, a wurin jana'izar Cif Kemi Nelson a cocin Tunawa da Archbishop Vinning, Ikeja, Legas. Kafin wasu su kara gishiri da yaji, bari in bayyana abin da ya faru.
"Ni da Sanata Tokunbo Abiru da Dakta Tunji Olowolafe mun isa wurin kusa lokaci guda kuma muka tafi mu gaisa da yar uwarmu, Sanata Oluremi Tinubu. Muna hada ido, muka gaisa kamar yadda aka saba kuma sai ta tambaye yi, 'Wato Bob Dee, ba za ka yi wa miji na kamfen ba ...?' Na yi murmushi cikin natsuwa kafin na bata amsa: "Ranki Ya Dade, A PDP na ke...' Bisa dukkan alamu bata ta ji dadin hakan ba kuma ta rika tuna min zumuncin da ke tsakani na da mijinta yayin da na ke kokarin kwantar mata da hankali."

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar Accord Party Ta Zabi Dan Siyasan Arewa Matsayin Mataimakin Shugaban Kasa

Momodu ya ce daga nan ya koma wurin zamansa ya rika tunanin yadda yan jarida suka rika tambayarsa idan zai fita daga PDP idan bai samu tikitin takara ba, kuma ya amsa musu da cewa a'a.

Ya cigaba da cewa yana kaunar Asiwaju Bola Tinubu kuma sun dade suna zumunci amma kaunar da ya ke yi wa Najeriya ya fi abotansa da shi hakan yasa ya ke PDP don taimakawa a ceto Najeriya.

Tinubu: Abin Da Yasa Na Zabi Musulmi A Matsayin Abokin Takara Na A 2023

A wani rahoton, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben 2023 ya kare zabinsa na Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takara, Daily Trust.

Kafin bayyana Shettima a matsayin mataimaki, siyasar kasar ta dauki zafi kan batun zaben yan takara masu addini iri daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel