2023: Jam'iyyar Accord Party Ta Zabi Dan Siyasan Arewa Matsayin Mataimakin Shugaban Kasa

2023: Jam'iyyar Accord Party Ta Zabi Dan Siyasan Arewa Matsayin Mataimakin Shugaban Kasa

  • Jam'iyyar Accord Party ta zabi tsohon SSG na jihar Zamfara, Bello Bala Maru matsayin mataimakin shugaban kasa
  • Muhammadu Nalado, shugaban jam'iyyar Accord na kasa ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis 25 ga watan Agusta
  • Farfesa Imumolen, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ya yi maraba da zabin Maru, ya kuma ce yana kyautata zaton za su ci zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Accord Party, Farfesa Christopher Imumolen ya zabi tsohon sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Bello Bala Maru a matsayin abokin takararsa, The Cable ta rahoto.

Sanarwar da aka raba wa manema labarai a ranar Alhamis ta ce jam'iyyar ta zabi dan siyasan daga Arewa maso Yamma ne bayan tuntuba da kuma lura da karfin fada a ji da ya ke da shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Rufe Sabuwar Ofishin NNPP A Borno, An Kuma Kama Shugaban Jam'iyyar

Bello Maru
Tsohon SSG Na Zamfara Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke magana wurin taron, shugaban Accord Party na kasa, Muhammad Nalado, ya ce bisa dukkan alamu jam'iyyar ta yi zabi nagari da zai hada kan yan Najeriya daga kudu da arewa.

Ya bayyana gamsuwarsa cewa jam'iyyar ce za ta samar da shugaban kasa da mataimaki a Najeriya a shekarar 2023, Vanguard ta rahoto.

Ya bayyana cewa da jam'iyyar Accord ne Najeriya ta samu yanci kuma ta samar da masu kishin kasa, yana mai kira ga matasa su rungumi Farfesa Imumolen wanda matashi ne ga kuma abokin takararsa dattijo mai hikima.

Martanin dan takarar mataimakin shugaban kasar na Accord

Dan takarar mataimakin shugaban kasar, ya yi godiya bisa zabensa da aka yi a matsayin wanda ya dace da aikin.

Ya ce amince ne bayan tuntuba na lokaci mai tsawo, sannan ya fito daga jiha wacce matsalar rashin tsaro ya addabe ta.

Kara karanta wannan

Daga karshe: NNPP ta yi magana game da yiwuwar hadewar Kwankwaso da Tinubu a 2023

Jawabin Farfesa Imumolen

A bangarensa, dan takarar shugaban kasar na Accord Party, Farfesa Imumolen ya ce jam'iyyarsu ce za ta lashe zaben shugaban kasa na 2023, tare da goyon bayan matasa da sauran yan Najeriya.

Ya yi maraba da abokin takararsa kuma ya ce ya dace da matsayin.

Abin Da Muka Tattauna Da Obasanjo, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP

Tunda farko, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na Accord Party, AP, Farfesa Christopher Imumolen ya bayyana abin da suka tattauna da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Vanguard ta rahoto cewa ba wannan bane karo na farko da mai fatan zama shugaban kasar ya ziyarci tsohon shugaban kasar.

Yayin ziyarar, hotuna sun nuna farfesan ya rusuna kan gwiwansa yayin da Obasanjo ke masa addu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel