Kiristocin APCn Arewa Sun Dage Dole a Ba Su Kujerar Mataimakin Tinubu

Kiristocin APCn Arewa Sun Dage Dole a Ba Su Kujerar Mataimakin Tinubu

  • Kiristoci daga Arewa ta Tsakiya sun tura wa shugaban kasa Muhammadu budaddiyar wasika game da tikitin Tinubu da Shettima
  • Ana ta kai ruwa rana a jam'iyyar APC tun bayan da jam'iyyar ta tsayar da Musulmi da Musulmi a takarar shugabancin kasa na 2023
  • Gwamna daga yankin Arewa ya ce Paparoma bai tanka masa ba game da goyon bayan Tinubu da Shettima da yake

FCT, Abuja - Kungiyar Kiristocin Arewa ta APC ta yi kira da a maye gurbin Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar a zaben shugaban kasa mai zuwa, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Tun kafin wannan hargirsi na kiristocin APC 'yan Arewa, an yi ta rade-radin cewa dan takarar APC Bola Ahmed Tinubu (Musulmi) zai zabi dan uwansa Musulmi a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan Arewa: Kamata ya yi Shettima ya hakura da takara da Tinubu saboda dalilai

Kiristocin Arewa sun nemi a kwace tikitin Kashim Shettima
Kiristocin APCn Arewa Sun Dage Dole a Ba Su Kujerar Mataimakin Tinubu | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Tinubu ya yi ta maza, ya ayyana Sanata Kashim Shettima (Musulmi) a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, lamarin da ya jawo cece-kuce da hargitsi daga al’ummar Kiristan kasar nan.

Wannan batu dai ya kara ta'azzara ne yayin da mabiya addinin kirista na jam'iyyar a jihohin Arewa ta Tsakiya shida suka yi watsi da mukamin daraktan yakin neman zaben shugaban kasa da aka baiwa gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu 'yan zanga-zanga daga kungiyar Matasa da Mata ta APC a Arewa ta Tsakiya sun yi gangami a Abuja domin nuna rashin jin dadinsu kan matakin da shugabannin jam’iyyar suka dauka na hada tikitin takarar Musulmi da Musulmi.

Daga ina 'yan zanga-zanga suka fito?

An ce wadannan masu zanga-zangar sun fito ne daga garuruwan Arewa ta Tsakiya da dama kamar Ilorin, Makurdi, Lafia, Minna, Jos, da makamantansu.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi-Musulmi: Paparoma bai ce na yi kuskuren marawa Tinubu da Shettima baya ba, inji Lalong

Wata wasika mai dauke da sa hannun shugabanta, Dauda Yakubu da sauran masu ruwa da tsaki, ta bayyana cewa akwai bukatar jam’iyyar ta hankalta, kada kuma ta jahilci cewa yankin Arewa ta Tsakiya ya taka rawar gani wajen ci gaban kasar nan.

Daga karshe ma, sun yarda cewa Kirista daga yankin Arewa ta Tsakiya ne ya fi dacewa da karbar kujerar takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben mai zuwa.

Wasikar ta bayyana cewa, kai tsaye tana jan hankali ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsoma baki domin tabbatar da yankinsu ya samu wannan tikitin.

A cewar wasikar:

"Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da magoya bayan jam'iyyar APC a fadin jihohin Arewa ta Tsakiya shida da suka hada da babban birnin tarayya Abuja sun matsa su rubuta wannan budaddiyar wasika zuwa ga shugaban kasa da kuma babban kwamandan rundunonin sojan tarayyar Najeriya."

Gwamna Lalong: Ina Alfahari da Jagorantar Tafiyar Tinubu da Shettima Duk da Ni Kiristan Katolika Ne

Kara karanta wannan

Zaben 2023: APC ta sanar da ranar da za ta fara gangamin yakin neman zaben Tinubu

A wani labarin, gwamna Simon Lalong na jihar Filato a ranar Laraba ya soki Kiristocin da ke adawa da amincewarsa ta zama babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na APC.

Lalong ya bayyana cewa a matsayinsa na kiristan Katolika da ya samu lambar yabo ta Paparoma, shi Paparoman bai ce masa abin da ya yi ba daidai bane.

Bayan fitowar Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya zabi tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa, rahoton Channels Tv.

Asali: Legit.ng

Online view pixel