Dalilin Da Yasa Ba Zan Yi Musu da Atiku Kan Zaɓo Gwamna Okowa Ba, Ortom

Dalilin Da Yasa Ba Zan Yi Musu da Atiku Kan Zaɓo Gwamna Okowa Ba, Ortom

  • Gwamnan jihar Benuwai ya ce ba zai tsaya gardama da ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ba kan zaɓen mataimaki
  • Da yake amsa tambayoyin manema labarai a Makuɗi, Ortom ya ce lamarin na yan gida ɗaya ne kuma za'a warware sabanin a cikin iyalai
  • Atiku ya yi iƙirarin cewa babu wata kuri'a da aka kaɗa ta bashi shawara ya ɗauki Wike, mutum uku aka gabatar masa ya zaɓi ɗaya

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, a ranar Litinin, ya faɗi dalilin da yasa ba zai yi musu da Atiku Abubakar ba game da zaɓo gwamna Ifeanyi Okowa na Delta a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP.

Tun da fari, Ortom ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasan da yin fatali da shawarin da kwamiti ya ba shi na ɗaukar gwamnan Ribas, Nyesom Wike, a matsayin abokin takara.

Kara karanta wannan

Zan fallasa komai game da Atiku don kowa ya san gaskiya, Gwamnan PDP ya fusata

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom.
Dalilin Da Yasa Ba Zan Yi Musu da Atiku Kan Zaɓo Gwamna Okowa Ba, Ortom Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa amma Atiku, a wata hira, ya bayyana ikirarin Gwamna a matsayin zancen da ba ƙamshin gaskiya kan zargin ya yi fatali da shawarin Kwamitin PDP.

Atiku ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ba'a kaɗa kuri'a ba, zan iya ba ka kwafin rahoton kwamitin. Kwamitin da ya gabatar da jerin mutum uku yana karkashin jagorancin gwamna Benuwai, Samuel Ortom, sun ba da shawarin mutun uku, ni kuma na zaɓi ɗaya."

Martanin Ortom ga Atiku

Gwamnan Benuwai ya bayyana cewa tuni suka warware lamarin a matsayin abun da ya shafi ƴan gida ɗaya.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a Makurɗi, ranar Litinin, Gwamna Ortom ya ce:

"Bana son yin gaddama da ɗan takarar mu na shugaban kasa, duk abun da ya faru, daidai ko kuskure na ɗauka. Mu iyali ɗaya ne, zamu lalubo hanyar da zamu warware matsalar."

Kara karanta wannan

Haɗin kan ƙasa da tsaron yan Najeriya zan sa a gaba, Buhari ya faɗi abinda zai yi bayan ya sauka mulki

Ortom ya ƙara da cewa tuni ɗan takarar shugaban kasan ya fara rarrashin gwamna Wike kan abubuwan da suka biyo bayan zaɓen fidda gwani.

"Baki ɗaya abin da nake son ganin an gudanar (game da gwamna Wike) Atiku ya yarda kuma sun fara tattauna wa tsakanin su."

A wani labarin na daban kuma Atiku, Tinubu sun gamu da cikas a kokarin gaje Buhari, wasu ɗaruruwan mambobin PDP da APC sun koma LP

Jam'iyyar LP wacce Peter Obi ke takarar shugaban ƙasa ta samu gagarumin goyon baya a babban birnin tarayya Abuja.

Yayin da ake gab da fara yaƙin neman zaɓe, ɗaruruwan mambobin APC da PDP a yankin Kuje sun sauya sheƙa zuwa LP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel