Adeleke, Shekarau, El-Rufai, wasu 23 da suka Hana Gwamnoni masu-ci yin tazarce

Adeleke, Shekarau, El-Rufai, wasu 23 da suka Hana Gwamnoni masu-ci yin tazarce

  • A watan nan ne Ademola Adeleke ya doke Gboyega Oyetola daga kan kujerar Gwamnan jihar Osun
  • Kafin Sanata Ademola Adeleke, an yi ‘Yan siyasan da suka hana Gwamnoninsu zarcewa a kan mulki
  • Wannan rahoto ya tattaro mana duka wadanda suka kafa tarihi a siyasa daga 1999 zuwa shekarar nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ga jerin nan da Legit.ng Hausa ta tattaro maku:

1. Ibrahim Shekarau

A 2003, Malam Ibrahim Shekarau ya yi takara a Kano a karkashin jam’iyyar ANPP, ya kuma doke Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso wanda yake kan karagar mulki a inuwar PDP.

2. Bukola Saraki

Dr. Abubakar Bukola Saraki ya lashe zaben Gwamna a jihar Kwara ne bayan doke Admiral Mohammed Lawal wanda shi ne Gwamna mai-ci a karkashin APP a lokacin.

3. Ibrahim Idris

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari ya shiga wata ganawa mai muhimmanci da Shettima da su Tinubu

A lokacin yana ANPP, Prince Abubakar Audu ya rasa tazarcensa ne a hannun Ibrahim Idris a 2003. Idris ya zarce a kan mulki, ya sake doke tsohon Gwamnan a zaben 2007.

4. Mohammed Danjuma Goje

Mohammed Danjuma Goje ne ya raba Abubakar Hashidu daga gidan gwamnatin Gombe. Tsohon Ministan tarayyan ya kawo karshen mulkin jam’iyyar ANPP a shekarar 2003.

5. Ali Modu Sheriff

Shi kuwa Abubakar Mala Kachallah ya bar jam’iyyarsa ta ANPP zuwa AD ne bayan da Sanata Ali Modu Sheriff ya doke shi wajen samun tikiti, ya kuma lashe babban zabe.

6. Chris Ngige

A zaben 2003, Chinwoke Mbadinuju ya sha kasa a jihar Anambra a hannun jam’iyyar APGA. Daga baya kotu ta karbe nasarar APGA, ta ba PDP mai mulki da Chris Ngige nasara.

7. Olusegun Agagu

Olusegun Kokumo Agagu ya yi gwamna a jihar Ondo a 2003 bayan ya kifar da Adebayo Adefarati. Daga baya kotu ta tunbuke Agagu, ta daura Olusegun Mimiko a kan mulki.

Kara karanta wannan

Dangote, Dantata da Jerin Kanawa 8 da ke cikin Sahun Masu kudin Najeriya

8. Olagunsoye Oyinlola

Zaben 2003 ya ba Ọlagunsoye Oyinlọla nasarar zama Gwamnan jihar Osun a karkashin jam’iyyar PDP da ya doke Bisi Akande. A karshen 2010 shi ma kotu ta ruguza zabensa.

9. Segun Oni

See Niyi Adebayo in Ekiti

Olusegun Oni ya yi gwamna a Ekiti na tsawon shekaru uku a PDP. Oni bai doke Gwamna mai-ci a zaben 2007 ba, amma ya dare karagar mulki ne bayan tsige Ayo Fayose.

10. Oserheimen Osunbo

Sanata Oserheimen Osunbor ya rike kujerar Gwamna na shekara daya da rabi a jihar Edo bayan ya doke Gwamna mai-ci. Osunbar yana cikin ‘yan PDP da suka karbe kujerun AD.

11. Rasheed Ladoja

Shi kuwa Rashidi Adewolu Ladoja ya yi mulki a PDP daga 2003 zuwa 2006 a sakamakon doke Lam Adesina. Bayan an tsige shi daga kujerarsa, ya koma har zuwa 2007.

12. Christopher Alao-Akala

Christopher Alao-Akala ya samu galaba a kan Rasheed Ladoja a zaben 2007, Akala yana cikin wadanda suka yi mulkin wa’adi daya a Oyo, yana da tarihin doke Gwamna.

Kara karanta wannan

Manyan Kudu sun yi watsi da APC, Tinubu, sun ki halartar bikin kaddamar da Shettima

13. Gbenga Daniel

Otunba Gbenga Daniel ne wanda ya dankara Segun Osoba da kasa a lokacin yana Gwamnan Ogun. Daniel ya yi shekaru takwas a ofis, daga baya sai aka ji ya koma APC.

Ademola Adeleke
Ademola Adeleke yana kamfe a Osun Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

14. Kayode Fayemi

Dr. Kayode Fayemi ya dare kujerar gwamna a Ekiti bayan doguwar shari’ar zabe tsakanin ACN da PDP a kotu. A 2010 aka rantsar da shi, kotu tayi waje da Injiniya Segun Oni.

15. Abdulaziz Yari

A dalilin komawarsa PDP daga jam’iyyar ANPP, Mamuda Aliyu Shinkafi ya rasa kujerar Gwamnan Zamfara a 2007 a hannun Abdulaziz Yari wanda ya yi zamansa a ANPP.

16. Tanko Al Makura

Aliyu Akwe Doma na jihar Nasarawa yana cikin wadanda sabuwar jam’iyyar CPC tayi wa lahani a zaben 2011. Tanko Al Makura ya karbe mulkin jihar daga hannun PDP.

17. Rochas Okorocha

Ikedi Ohakim ya yi mulkin wa’adi daya ne a jihar Imo domin ya sha kashi da ya sauya-sheka a 2011 a hannun Rochas Okorocha wanda ya nemi Gwamna a jam’iyyar APGA.

Kara karanta wannan

Rashin da'a: Mataimakan gwamna 5 da aka tsige su a Najeriya, amma kotu ta mayar dasu

Zabukan 2015 da bayan zaben

18. Nasir El-Rufai

Wanda ya doke Mai girma Ramalan Yero daga kujerar Gwamnan Kaduna shi ne Malam Nasir El-Rufai na APC. A karon farko PDP kenan da PDP ta rasa iko da jihar tun 1999.

19. Yahaya Bello

Yana matashinsa, Yahaya Bello ya zama gwamna a sakamakon doke Idris Wada na PDP da APC tayi a karshen 2015. Bello ya gaji nasarar Marigayi Abubakar Audu ne a zaben.

Siyasar 2019

20. Ahmadu Umar Fintiri

Gwamnan Adamawa, Jibrila Bindow ya gagara zarcewa a jam’iyyar APC a zaben 2019. Ahmadu Fintiri na PDP ya yi galaba a kan shi da kuri’ar da ba ta wuce 40, 000 ba.

21. Bala Mohammed

Sanata Bala Mohammed Abdulkadir na PDP ya doke Mohammed Abdullahi Abubakar na APC a jihar Bauchi a zaben 2019, tsohon Ministan ya yi nasara da ratar 15, 000.

22. Babajide Sanwo Olu

Akinwunmi Ambode ya bada mamaki a 2018 da ya rasa tikitin APC na Legas ga Babajide Sanwo-Olu mai kuri’u 970, 851, shi kuwa Gwamnan mai-ci ya samu kuri'u 70, 091 ne.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hotuna sun bayyana, Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja

23. Gboyega Oyetola

Gwamna Gboyega Oyetola shi ne a karshe a wannan jeri wanda duk da ya samu kuri’u 375, 027, ya rasa takarar tazarcensa a hannun Ademola Adeleke na PDP da ya samu 403,371.

Asali: Legit.ng

Online view pixel