Jiga-jigan APC za su tattauna game da babban taron gangamin jam'iyyar su
- Jiga-jigan APC za su tattauna game da babban taron gangamin jam'iyyar su
- Za su tattauna ne a ranar Laraba mai zuwa a hedikwatar jam'iyyar dake a Abuja.
Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki da suka hada da kwamitin gudanarwa na kasa, gwamnonin jam'iyyar da ma wasu manyan masu fada a ji a jam'iyyar za su yi wata tattaunawa a ranar Laraba mai zuwa a hedikwatar jam'iyyar dake a Abuja.
KU KARANTA: Yan bindiga sun tafka ta'asa a jihar Benue
Jam'iyyar ta sanar da cewa wannan taron dai ana sa ran su tattauna ne game da babban taron gangamin jam'iyyar da ke tafe da kuma sauran shire-shiren jadawalin gudanar da jam'iyyar.
Legit.ng ta samu a wani labarin cewa Shugaban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, watau Prince Uche Secondus ya bayyana cewa a halin yanzu 'yan kasar nan na fuskantar wani irin bakin mulki mai cike da son kai da rashin adalci a karkashin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari da kuma jam'iyyar All Progressives Congress karara.
Mista Uche Secondus ya yi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wasu 'yan majalisun tarayyar Najeriyar a karkashin inuwar jam'iyyar su a ranar Talatar da ta gabata ne a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng