PDP ta kai INEC Kotu, ta bukaci a haramtawa Tinubu da Peter Obi neman Shugaban kasa

PDP ta kai INEC Kotu, ta bukaci a haramtawa Tinubu da Peter Obi neman Shugaban kasa

  • Jam’iyyar PDP ta na karar masu neman takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyun APC da na LP
  • Bola Tinubu da Peter Obi sun canza sunayen wadanda za su zama abokan takararsu a 2023
  • Za a soma yin shari’ar ne a babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja da zarar an sa lokaci

Abuja - Jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar da karar INEC a kotu, ta na neman tursasawa hukumar zaben ta hana APC da LP shiga zaben shugaban kasa.

Punch ta ce Lauyoyin PDP su na so Alkali ya hana ‘dan takaran APC, Bola Tinubu da na LP, Peter Obi damar canza abokan takararsu a zaben 2023 mai zuwa.

Jam’iyyar PDP ta kai kara ne a babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja a tsakiyar makon nan.

Kara karanta wannan

Bayan gaza samun tikitin Shugaban kasa, Jigon APC ya gagara samun tikitin Sanata

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1016/2022, ana kalubalantar maye guraben Doyin Okupe da Kabir Masari da Kashim Shettima da Datti Baba-Ahmed.

Lauyoyin jam’iyyar hamayyar sun kuma roki Alkali ya haramtawa Tinubu da Obi takara a 2023 muddin ba su dawo da Masari da Dr. Okupe a tikitinsu ba.

Za ayi shari'a da INEC, LP, APC

Rahoton ya ce wadanda aka hada a karar sun hada da hukumar zabe na kasa, jam’iyyun APC da LP, Bola Tinubu, Kabir Masari, Peter Obi da Doyin Okupe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai neman Shugaban kasa a APC
Bola Tinubu a Osun Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Lauyoyin PDP da suka shigar da kara su na so Alkali ya fassara sashe na 142 (1) na tsarin mulki da sassa na 29(1), 31 da 33 na dokar zabe na kasa na 2022.

Haka zalika lauyoyin su na so ayi la’akari da jadawalin INEC wajen duba halaccin Tinubu da Obi su canza sunan ‘yan takarar mataimakan shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Jerin shahararrun Taurari 6 da suka zama ‘Yan takaran siyasa a zaben 2023

PDP ta hakikance a kan cewa ‘yan takaran na APC da LP da ake kara, ba su da damar da za su maye guraben abokan takaran 2023 da suka dauka tun farko.

Idan PDP ta yi nasara a shari’ar, Alkali zai yi hana Bola Tinubu da Peter Obi yin takara muddin suka canza sunan wanda za su yi masu takarar mataimaki.

Da farko APC ta tsaida Kabiru Masari ne kafin a canza shi da Kashim Shettima, shi kuma Doyin Okupe ya bada sunansa kafin a kawo Yusuf Datti Ahmed.

Osinbajo ya bar APC?

Dazu aka ji labari mai taimakawa Yemi Osinbajo wajen hulda da jama’a, Laolu Akande ya yi bayani a kan takardar da ake cewa mai gidansa ya bar APC.

Akande ya fadawa manena labarai cewa Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, bai rubuta wani abu sam mai kama da wannan ba.

Kara karanta wannan

Tikitin Tinubu/Shettima: Adamu Garba ya sake komawa jam’iyyar APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel