‘Dan Majalisar da ke wakiltar yankin Atiku Abubakar ya tsere zuwa jam’iyyar NNPP

‘Dan Majalisar da ke wakiltar yankin Atiku Abubakar ya tsere zuwa jam’iyyar NNPP

  • Hamman tukur Yettusuri mai wakiltar mazabar Jada a majalisar dokokin jihar Adamawa ya bar PDP
  • ‘Dan majalisar ya tabbatar da wannan da ya ziyarci sakatariyar jam’iyyar ta NNPP da ke garin Yola
  • Hon. Yettusuri ya na wakiltar yankin Atiku Abubakar kuma shi ne shugaban masu rinjaye a majalisa

Adamawa - A yammacin Talata, 5 ga watan Yuli 2022, labari ya zo mana daga hukumar dillacin labarai na kasa cewa Hammatukur Yattasuri ya bar PDP.

Honarabul Hammatukur Yattasuri wanda shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Adamawa ya fice daga jam’iyyar PDP mai mulkin Adamawa.

Da yake jawabi a wajen wani taro a garin Yola, ‘dan majalisar ya ce ya fita daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP ne domin ya iya taimakawa al’ummarsa da kyau.

Kara karanta wannan

Machina ya sanar da INEC cewa ana kokarin fitar da wasikar bogi kan janye wa Lawan

Hon. Yattasuri ya yi alkawari mutanen mazabarsa za su sha romon damukaradiyya da kyau idan har ya yi nasarar lashe zaben ‘dan majalisar wakilan tarayya.

Sahara Reporters ta ce NNPP ta ba ‘dan siyasar tikitin takarar ‘dan majalisa na mazabar da Atiku Abubakar ya fito watau na Jada/ Toungo/Ganye/MayoBelwa.

‘Dan Majalisar PDP
Majalisar dokokin Adamawa Hoto: @AdamawaAssembly
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin komawa ta NNPP - Yettusuri

Politics Digest ta rahoto Yettusuri yana mai cewa ya rabu da su Atiku Abubakar, ya bi NNPP ne domin ya hada-kai da na kwarai da nufin a gyara Najeriya.

'Dan majalisar ya zargi PDP da kama-karya, wanda ya ce hakan zai kai ga wargajewar jam'iyyar da ya bari wanda ke da mulki da rinjaye a majalisar dokoki.

Daily Nigerian ta ce ‘Dan majalisar jihar zai nemi kujerar majalisar tarayya a karkashin NNPP.

Jam’iyyar NNPP ta ji dadi

Kara karanta wannan

Jam’iyyar Labor Party ta lallaba wajen mutanen Zakzaky, ta na nemawa Peter Obi kuri’u

Sakataren jam’iyyar NNPP na shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, Hamman Ribadu, ya yi jawabi a wajen bikin da aka shirya domin karbar ‘dan majalisar.

Ribadu yake cewa shugaban marasa rinjayen na majalisar Adamawa ya shigo NNPP a lokacin da ake bukata, ya ce za jam’iyya za ta bashi gudumuwar da ake nema.

Kamar yadda Saidu Salmana ya yi bayani dazu da rana, ya ce Hon. Hammatukur Yattasuri ‘dan siyasa ne mai amana, hali mai kyau da kuma dinbin magoya baya.

Salmata wanda shi ne shugaban NNPP a karamar hukumar Jada ya jinjinawa sabon kamun, ya ce ‘dan majalisar ya yi dabara da ya shigo NNPP mai kayan marmari.

Tinubu: IGP zai kare kan shi a kotu

An ji labari kwai yiwuwar Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba ya je gaban Alkali saboda ya ki kai ‘Dan takaran APC a 2023, Asiwaju Bola Tinubu kotu

Ana zargin wanda APC ta ba takarar shugaban kasa yana da ta-cewa a kotu a kan batun takardunsa, wanda lamarin ya kai an taba bincikensa a shekarar 1999.

Kara karanta wannan

Kungiyar da ta sayawa Tinubu Fom din N100m, ta ce Elrufai take goyon bayan ya zama mataimaki

Asali: Legit.ng

Online view pixel