Jam’iyyar Labor Party ta lallaba wajen mutanen Zakzaky, ta na nemawa Peter Obi kuri’u

Jam’iyyar Labor Party ta lallaba wajen mutanen Zakzaky, ta na nemawa Peter Obi kuri’u

  • ‘Dan takarar Jam’iyyar LP a jihar Kaduna, ya ce sun zauna da Islamic Movement in Nigeria (IMN)
  • Shunom Adinga ya nemi shugaban IMN ya marawa LP baya a matakin jiha da kasa a zaben 2023
  • A cewar ‘dan takarar gwamnan na Kaduna, jam’iyyar su ta na jawo wadanda aka fusata a jikinta

Kaduna - ‘Dan takarar Labour Party (LP), Shunom Adinga, ya bayyana cewa sun tuntubi jagoran kungiyar IMN, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da mutanensa.

Shunom Adinga yake cewa sun yi zama da Sheikh Ibraheem El-Zakzaky ne domin malamin ya marawa Peter Obi baya a zaben shugabancin Najeriya a 2023.

Tribune ta rahoto Adinga yana mai cewa shi ma zai so jagoran na IMN ya goyi bayan burinsa na zama gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar adawar.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

‘Dan takarar gwamnan na 2023 ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi hira ta musamman da manema labarai a karshen makon da ya gabata a garin Kaduna.

A cewar Adinga, ya shiga takarar gwamna ne saboda burin yi wa al’umma jagoranci na adalci da inganta rayuwarsu tare da bunkasa tattali da kawo cigaba.

LP ta na jawo wadanda aka batawa rai

‘Dan siyasar yake cewa su na kokarin shawo kan bangarorin da aka fusata ko suke ganin an yi masu ba daidai ba, daga ciki akwai ‘yan kungiyar nan ta IMN.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

El-Zakzaky
Shugaban IMN, Ibraheem Yakub El-Zakzaky Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC
“Mu na kokari sosai na jawo fusatattun bangarorin da ke cikin al’umma irinsu ‘Yan Shi’a da El-Zakzaky domin su marawa LP baya.”
“Mun tuntube su, kuma mun yi magana sosai a kan abubuwan da suka shafi dukkaninmu.”
“Sannan kuma mun fahimci juna a game da gwamnatin Peter Obi da za a rantsar domin tabbatar da cewa an farfado da tattalin arziki.”

Kara karanta wannan

Tsohon Na Hannun Daman Kwankwaso Ya ki Yarda Ya yi Aiki a Kwamitin Kamfen Peter Obi

“Mu na bakin kokari na tabbatar da cewa an shigo da kowane bangare da ya yi fushi, domin mu cin ma manufar da mu ke da buri.”

- Shunom Adinga

Daily Trust ta rahoto Aduhi ya ce duk Najeriya babu wata jam’iyyar da ta kai su farin jini saboda an kafa LP ne domin ma’aikata, kuma sun fi ‘yan siyasa yawa.

APC ta tsaida ‘Yar takara

A jiya aka samu rahoto Sanata Uba Sani ya yi bayanin dalilin sake daukar Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ta zama Mataimakiyar Gwamnan Kaduna a zaben 2023

Da yake jawabi a ranar Litinin, ‘Dan takaran na jam’iyyar APC ya ce ganin irin kokarin da ta yi, manyan jiha sun bada shawarar a tafi da mataimakiyar gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel