Ban janyewa Ahmad Lawan ba, duk takardar da aka gani na janyewa bogi ne - Machina

Ban janyewa Ahmad Lawan ba, duk takardar da aka gani na janyewa bogi ne - Machina

  • Machina ya zargi wasu manyan jam'iyyar APC da kokarin amfani da wasikar bogi wajen cewa ya janyewa Ahmed Lawan daga takara
  • Jam'iyyar APC ta maye gurbin sunan Machina da suna Ahmed Lawan a cikin jerin sunayen da ta aikawa hukumar INEC
  • Machina ya dau alwashin kwato hakkin sa a kotu da tabbatar da hukumar INEC ba canza sunan sa da sunan wani ba

Jihar Yobe - Wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa, Bashir Machina, ya sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan wani shiri da yake zargi da an sanya hannun sa kan wata wasikar bogi, inda ya bayyana ya janye daga takara ya share fage ga shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan kamar yadda jaridar THISDAY ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Saba alkawari: Ta karewa APC a Sokoto, 'yan kasuwa sun yi watsi da ita sun koma PDP

Mai magana da yawun dan takarar Sanata na APC a Yobe ta Arewa, Husaini Mohammed Isah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labaran THISDAY a ranar Talata a Abuja.

Isah ya yi mamakin dalilin da ya sa wasu jiga-jigan jam’iyyar za su hada baki su kirkiro wata wasikar janyewa da ake zargin ta fito daga Machina a lokacin da dan takarar ya riga ya rubuta kwamitin aiki na jam’iyyar APC na kasa cewa ba zai janye daga takara ba.

Machi
Machina ya sanar da hukumar INEC kan takardar janyewa Lawan na jabu FOTO : PUNCH
Asali: UGC

Machina ya na kokarin kwato hakkin sa daga hannun shugabancin jam’iyyar APC.

Jam’iyyar dai, a cikin jerin ‘yan takarar da aka aika wa INEC, ta maye gurbin sunan Machina da sunan shugaban majalisar dattawa, Lawan, wanda bai shiga aikin ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Jam’iyyar Labor Party ta lallaba wajen mutanen Zakzaky, ta na nemawa Peter Obi kuri’u

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta tabbatar da cewa Machina ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC na mazabar Yobe ta Arewa da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayun 2022.

A rahoton jaridar THISDAY ta samu daga hukumar INEC a Abuja ya nuna cewa Machina ya samu kuri’u 289 daga cikin 300 da suka halarci zaben.

Wannan rahoton ya dakile duk wani ikirari da jam’iyyar APC ta yi na cewa shugaban majalisar dattawa, Lawan ne ya lashe tikitin jam’iyyar.

Binciken da jaridar THISDAY ta gudanar ya nuna cewa Machina zai shigar da kara kotu dan kwato hakkin sa da tabbatar da hukuma INEC bata canza sunan shi da na wani ba.

Hajjin Bana: Har yanzu maniyyatan Najeriya 8,000 suna gida

A wani labari, Najeriya : Duk da Karin wa’adin diban maniyyatan Najeriya zuwa kasa mai tsarki da gwamnatin Saudiyya tayi, har yanzu akwai rashin tabbas akan makomar maniyyata da dama kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Sa’o’i 24 ya rage wa’adin da Saudiya ta karawa Najeriya ya cika amma Sama da maniyyata 8,000 ba su san makomar su ba, yayin da suke jiran jirgin da zai kwashe su zuwa kasar

Asali: Legit.ng

Online view pixel