Kwankwaso Bai Zagi Kudu Maso Gabas Ba, Ba A Fahimce Shi Bane, Shugaban NNPP

Kwankwaso Bai Zagi Kudu Maso Gabas Ba, Ba A Fahimce Shi Bane, Shugaban NNPP

  • Shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, Rufai Ahmed Alkali ya ce dan takararsu Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai zagi mutanen Kudu maso gabas ba
  • Alkali ya yi karin haske ne a kan kalaman da aka danganta da Kwankwaso na cewa yan kudu maso gabas sun kware a kasuwanci amma sune na baya a siyasa
  • Shugabannin na NNPP ya ce Kwankwaso ya dade yana nuna muhimmin rawar da mutanen Igbo suka taka a siyasar Najeriya don haka ba raina su ya yi ba kuma yana bukatar kuri'ar kowa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rufai Ahmed Alkali, shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, na kasa ya ce kalaman da aka danganta da dan takarar shugaban kasar jam'iyyar, ba a fahimce su ba, The Cable ta rahoto.

A ranar Asabar, Kwankwaso ya ce yana bawa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party, 'muhimmiyar dama' na zama mataimakinsa.

Kara karanta wannan

'Yan a mutun Peter Obi: A bar maganar maja tsakanin Kwankwaso da Peter Obi

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso Bai Zagi Kudu Maso Gabas Ba, Ba A Fahimce Shi Bane, Shugaban NNPP. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Idan ma abokina [Peter Obi] yana son ya amince ya zama mataimakina, wasu mutanen kudu maso gabas ba za su amince ba, wannan ba dabara bace mai kyau," in ji shi.
"Wannan muhimmiyar dama ne, idan ta wuce su, abin ba zai yi kyau ba."

Martanin Alkali

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Alkali ya ce NNPP ba ta raina ko wane bangare na kasar nan ba don wani dalili.

"Dr. Mohammed Rabiu Musa Kwankwaso, yayin kaddamar da shugabannin jam'iyyar a Jihar Gombe a makon da ta gabata, an ambato ya ce mutanen Kudu maso Gabas (Igbo) sun kware a kasuwanci amma suna na baya a siyasa a Najeriya," in ji shugaban na NNPP.
"Maganar ta janyo rashin jin dadi a wasu bangarorin Najeriya, musamman tsakanin Kudu maso Gabas da NNPP.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya sun gaji da APC, Kwankwaso ya ce ya hango karshen APC

"Amma, a matsayinmu na jam'iyya mai son kawo canji a kasa, munyi imanin babu wani dan Najeriya daga yanki, kabila, ko addini da ba shi da muhimmanci wurin kawo canjin da ake bukata a kasar.
"NNPP na son fayyace cewa ba a fahimci kalaman da dan takarar shugaban kasarta Sanata Kwankwaso ya furta bane, don dan takarar shugaban kasar ya sha nanatawa cewa Igbo na kan gaba wurin samun yancin Najeriya, kuma suka samar da shugaban kasa na farko, Dr Nnamdi Azikwe, shugaban majalisa na farko, Dr Nwafor Orizu, tsohon mataimakin shugaban kasa, Dr Alex Ekwueme, tsaffin shugabannin majalisa hudu daga 1999 zuwa yau da wasu manyan masu rike da mukaman siyasa.
"NNPP a matsayinta na jam'iyyar da za ta yi takara a 2023 tayi imanin kamar sauran jam'iyyu tana da abin da ake bukata don kawo sauyi a kasar don haka ba za ta ware ko wane yanki ba ko mutanen jam'iyya."

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso bai cire ran hada-kai da Peter Obi ba, duk da 'Yan hana ruwa gudu

Shugaban jam'iyyar ya ce jam'iyyar na bukatar kuri'un dukkan yan Najeriya.

Babu Wannan Maganar: NNPP Ta Karyata Rade-Radin Kwankwaso Ya Zama Mataimakin Obi

A wani rahoton, jam'iyyar NNPP, ta yi martani kan wasu rahotanni a kafafen watsa labarai cewa dan takarar shugaban kasarta, Rabiu Kwankwaso, zai iya zama mataimakin dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi.

Jam'iyyar ta bayyana rahoton a matsayin "abin kunya da rashin gaskiya", rahoton The Punch.

Dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso, cikin wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya ce ana tattaunawa don duba yiwuwar maja tsakanin jam'iyyarsa da Labour Party.

Asali: Legit.ng

Online view pixel