Babu Wannan Maganar: NNPP Ta Karyata Rade-Radin Kwankwaso Ya Zama Mataimakin Obi

Babu Wannan Maganar: NNPP Ta Karyata Rade-Radin Kwankwaso Ya Zama Mataimakin Obi

  • Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta karyata cewa dan takararta Rabiu Musa Kwankwaso zai yi wa Peter Obi na Labour Party mataimaki
  • Dr Agbo Major, sakataren watsa labarai na NNPP ya ce labarin abin kunya gare su kuma babu wani kamshin gaskiya a cikinsa
  • Major ya tabbatar da cewa jam'iyyar NNPP tana tattaunawa kan yiwuwar maja da Labour Party amma har yanzu ba a cimma wata matsaya ba

Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, a ranar Lahadi ta yi martani kan wasu rahotanni a kafafen watsa labarai cewa dan takarar shugaban kasarta, Rabiu Kwankwaso, zai iya zama mataimakin dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi.

Jam'iyyar ta bayyana rahoton a matsayin "abin kunya da rashin gaskiya", rahoton The Punch.

Dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso, cikin wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya ce ana tattaunawa don duba yiwuwar maja tsakanin jam'iyyarsa da Labour Party.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Zanga-zanga ta barke a sakateriyar APC saboda adawa da zabin Tinubu

Peter Obi da Kwankwaso.
NNPP Ta Karyata Rade-Radin Kwankwaso Ya Zama Mataimakin Obi. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da cewa Kwankwaso bai ambaci cewa shi ko Obi zai zama mataimaki ba, ya ce majar za ta yi tasiri gabannin babban zaben 2023.

Amma, NNPP, cikin sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaranta na kasa, Dr Agbo Major, ta ce jam'iyyar ta samu labarai cewa Kwankwaso zai iya zama mataimakin Obi.

Ya ce:

"NNPP bata taba cewa dan takarar shugaban kasarta, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, zai iya amincewa ya zama mataimakin Peter Obi a Labour Party ba. Rahoton ba gaskiya bane kuma abin kunya ne ga jam'iyyarmu, dan takararta, Kwankwaso da miliyoyin magoya bayanta a Najeriya da kasashen waje, ya kuma bukaci yan jarida su rika bincika labari kafin su wallafa don kaucewa hada rikici a kasa gabanin babban zaben 2023.
"A matsayinmu na tafiya ta mutane da yawa, NNPP ta amince cewa tana tattaunawa da Labour Party don inganta jam'iyyar kasar a yayin da muke kokarin ganin samar da sabuwar Najeriya da jam'iyyar ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Ba ku da tsari: Dan kashenin Jonathan ya fice daga PDP, ya caccaki tsarin jam'iyyar na 2023

"Jaridar Sunday Trust ta bayyana a rahotonta; "An tambaya ya tabbatar da batun yiwuwar hadin kai, Major (Agbo) ya ce ana tattaunawa kuma ba ya son ya yi hasashe." Idan sakataren jam'iyyar na kasa ya ce "ana tattaunawa kuma baya son yin hasashe," ta yaya jaridar ta gano cewa Kwankwaso zai iya yiwa Obi mataimaki?
"NNPP na girmama yan jarida a matsayinsu na masu saka idanu a kasa kuma manyan masu ruwa da tsaki a harkar demokradiyya kuma ta bukaci su rika tabbatar da rahotanni kafin su wallafa kamar yadda dokokin aikinsu ya tanada. Tare za mu gina demokradiyya mai karfi da al'umma ta gari."

Legit.ng Hausa ta samu ji ta bakin Kwamared Ibrahim Danlami Kubau, dan takarar kujerar majalisar dokoki na tarayya na mazabar Ikara/Kubau don jin ra'ayinsa game irin hadin kan da ya ke ganin ya dace a yi tsakanin NNPP da Labour Party, LP.

Kubau ya fara da cewa yana ganin hadin kan tsakanin jam'iyyun biyu zai iya zama abin alheri duba da cewa jagorarin jam'iyyun biyu mutane ne da ke fatan ganin sabuwar Najeriya wacce za ta yi wa yan kasa adalci ta kuma samar musu ababen more rayuwa da tsaro da sauransu.

Kara karanta wannan

Kawancen NNPP-LP: Kwankwaso zai iya komawa mataimakin Peter Obi a zaben 2023

Sai dai ya ce bisa al'adar siyasa da kuma adalci, bangare da ke da magoya mafi rinjaye ne ya kamata ya yi jagoranci inda ya yi ikirarin cewa jam'iyyarsu ta NNPP na da mambobi masu katin zabe ya yawansu fi haura miliyan 12.

Ya kuma kara da cewa ba za a kwatanta kwarewar Kwankwaso ba da Obi a bangaren shugabanci da jagoranci idan an duba cewa jagoran na Kwankwasiya ya yi gwamna sau biyu, ya yi sanata, ya kuma yi ministan tsaro yayin da shi kuma Obi gwamna kawai ya yi sau biyu.

"Ina ganin idan har za a yi adalci toh Obi ne ya kamata ya zama mataimakin Kwankwaso duba da cewa NNPP ta fi LP yawan mabiya sannan ko bangaren kwarewa da jajircewa a mulki, Kwankwason na gaba," in ji shi.

Kwankwaso: Na tabbata Zan Yi Nasara, Ba Zan Janye Wa Atiku Ko Tinubu Ba

A wani rahoton, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya ce ba zai janye wa kowa takararsa ba har da yan takarar manyan jam'iyyun APC da PDP, wato Bola Tinubu da Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kwankwaso ya tabbatar da cewar suna kan tattaunawa da Peter Obi don hada gwiwar NNPP da LP

Jagoran na Kwankwasiyya ya bayyana hakan ne cikin wata hira ta musamman da ya yi da wakilin Jaridar The Punch, Abiodun Sanusi.

Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya ce tafiyar Kwankwasiya ta bazu dukkan sassan Najeriya kuma ya yi farin cikin ganin an ratabba hannu kan sabuwar dokar zabe don hakan na nufin zai yi wuya a murde zabe kamar yadda aka saba yi a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel