Zaben fidda gwani: Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Yobe, yan takara 8 sun tunkari kotu

Zaben fidda gwani: Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Yobe, yan takara 8 sun tunkari kotu

  • Yan takara takwas karkashin APC a jihar Yobe sun shiga kotu kan yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar
  • Hakan na zuwa ne yayin da rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar mai mulki reshen jihar ke kara kamari
  • Fusatattun yan takarar basu gamsu da sakamakon zaben fidda gwanin da aka gudanar ba a watan Mayu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yobe - Rikicin cikin gida ya barke a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Yobe yayin da fusatattun yan takara takwas suka dauki matakin kai kara kotu.

Yan takarar basu gamsu da sakamakon zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar na mazabun jiha da ta tarayya ba, Daily Trust ta rahoto.

Tuni dama takaddama ta kaure kan mamallakin tikitin APC na kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa, yayin da sunan shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya bayyana a jerin sunayen sanatocin da jam’iyyar ta mikawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.

Kara karanta wannan

Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

Mutum rike da tutar APC da tsintsiya
Zaben fidda gwani: Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Yobe, yan takara 8 sun tunkari kotu Hoto: APC
Asali: Twitter

Lawan dai ya yi takarar tikitin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki amma ya sha kaye a hannun tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Tinubu a zaben fidda gwani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bashir Sheriff Machina, wanda ya lashe zaben fidda gwanin da aka gudanar a Gashua a ranar 28 ga wayan Mayun 2022, ya ki janyewa Lawan sannan ya kalubalanci hukuncin jam’iyyar a gaban kotu.

Sai dai kuma, wani dan takarar kujerar ta sanata mai wakiltan Yobe ta arewa, Abubakar Abubakar Jinjiri, ma ya tafi kotu don kalubalantar cire sunansa a yayin zaben fidda gwanin.

An shigar da kararraki takwas a gaban Justis Fadima Murtala Aminu ta babbar kotun tarayya da ke Damaturu.

Suna kalubalantar sakamakon zaben fidda gwanin APC a mazabun Fika/Ngalda, Goya/Ngeji, Nangere, Bade ta yamma, Jakusko, Potiskum ta tsakiya, Bade Jakusko da kuma yankin Yobe ta arewa.

Kara karanta wannan

Mutanen Tinubu sun fara zawarcin jam’iyyun da basu da yan takarar shugaban kasa

Kotu ta saka ranar 21 ga watan Yulin 2022 don sauraron karar, rahoton Sahara Reporters.

Wani karin sanatan APC ya bi sahu, ya fice daga jam'iyyar

A wani labarin kuma, mun ji cewa yayin da jam'iyyar APC ke kokarin ɗinke barakar da ke kwashe mata Mambobi a majalisar Dattawa, Sanata Godiya Akwashiki, mai wakiltar mazaɓar Nasarawa da arewa ya fice daga jam'iyya mai mulki.

Daily Trust ta ruwaito cewa Akwashiki ya sanar murabus daga APC ne a wurin kaddamar da aikin gina hanyar Nassarawa Eggon/ Galle, da ke ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon, ranar Litinin.

Ɗan majalisar tarayya ya kafa hujja da zargin jirkita sunayen Deleget a matsayin dalilin da ya sa ya ɗauki matakin ficewa daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel