Kano: A Karon Farko An Samu Kakakin Majalisa Mace A Majalisar Yara

Kano: A Karon Farko An Samu Kakakin Majalisa Mace A Majalisar Yara

  • An samu mace ta farko, Hauwau Ibrahim Mohammed wacce ta zama kakakin majalisar yara na Jihar Kano
  • Hauwa Mohammed ta yi nasarar zama kakakin majalisar ne a zaben da ta lashe da kuri'u 38 sai mai biye mata Sadiq Mohammed Ghali ya samu kuri'u 30
  • Gwamnatin Jihar Kano ce ta shirya zaben tare da tallafin Expanding Social Protection for Inclusive Development, ESPID and Rule of Law and Anti-Corruption, RoLac

Kano - Wata daliba mai shekaru 16 daga Kano Capital Girls Schools a Jihar Kano, Hauwau Ibrahim Muhammad a ranar Laraba ta zama kakakin majalisa mace ta farko a majalisar yara zubi na 4 a jihar.

Hauwau, dalibar aji na 2 a babban sakandare yar asalin karamar hukumar Nasarawa ta lashe zaben ne bayan samun kuri'u 38 ta doke mai biye da ita, Sadiq Muhammad Ghali daga GSS, Gwale wanda ya samu kuri'u 30, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari'ar Musulunci Ta Ce A Bawa Abubakar Masauki a Gidan Yari Saboda Dage Wa Wata Gyale Ba Da Izininta Ba

Hauwa'u Mohammed.
Kano: A Karon Farko An Samu Kakakin Majalisa Mace A Majalisar Yara. Hoto: @Vanguardngr.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kazalika, Asiya Dahiru Ismail, wata daliba mace daga GGASS a karamar hukumar Danbatta ta zama mataimakiyar kakakin majalisar idan ta samu kuri'u 39.

Jami'in zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta na Jihar Kano, KANSIEC, Najib Bashir Musa ne ya jagoranci zaben wanda masu saka ido daga Ma'aikatar Tarayya da Jiha ta Harkokin Mata, Jami'an Tsaro da Kungiyoyin Al'umma da yan jaridu da sauransu suka sanya ido a kai.

Musa ya ce yara guda 81 suka yi rajista kuma suka kada kuri'a a zaben.

"Akwai kujeru guda 10 da aka yi zabe. Muna da jimillar masu zabe da suka yi rajista guda 81.
"Jimillar kuri'un da aka kada wa yan takarar 795 ne. Jimillar kuri'u masu kyau 780, yayin da marasa kyau kuma 15," in ji Musa.

Sauran manyan jami'an majalisar da aka zaba sun hada da Mustapha Sunusi Sani a matsayin jagoran majalisa, Habiba Aliyu (mataimakin jagoran majalisa), Muhammad Yasin (babban bulaliyar majalisa), Hamza Nasiru Ado (mataimakin bulaliya), Ummulkhair Mahmud (Magatakarda), Ibrahim Abdullahi (Mataimakin Magatakarda), Hauwa’u Nasir Nuhu da Hassan Abubakar Mai rike sandan majalisa da mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Dalibai Guda 15 Sun Ci Maki 1 Kacal a Jarrabawar Da NECO Ta Shirya, Yar Sokoto Ta Fi Kowa Cin Maki

Yaran sun fito ne daga makarantun kananan hukumomin jihar Kano 44, shekarunsu kuma daga 12 zuwa 16.

Gwamnatin Jihar Kano ce ta shirya zaben da tallafi daga Expanding Social Protection for Inclusive Development, ESPID and Rule of Law and Anti-Corruption, RoLac.

A jawabinta na nasara, sabuwar kakakin majalisar, Hauwau Ibrahim Muhammad ta yi alkawarin aiki da kowa wurin yin ayyukanta a matsayin sabuwar kakakin majalisar.

Ta kuma ce shugabancinta zai inganta halin da yara ke ciki a jihar Kano.

Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.

Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon gwamnan Ribas da Filato na mulkin soja, Kanal Shehu, ya rasu

Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.

Asali: Legit.ng

Online view pixel