Kano: Kotun Musulunci Ta Ce A Bawa Abubakar Masauki a Gidan Yari Saboda Dage Wa Wata Gyale Ba Da Izininta Ba

Kano: Kotun Musulunci Ta Ce A Bawa Abubakar Masauki a Gidan Yari Saboda Dage Wa Wata Gyale Ba Da Izininta Ba

  • Kotun shari'a ta bada umurnin a bawa wani Badamasi Abubakar masauki a gidan gyaran hali bayan ya amsa laifin dage wa wata yarinya gyale
  • Sufeta Abdul Wada, dan sanda mai gabatar da kara ya ce wata Summaiya Abdul da ke zaune a Marke Hotoro Quarters ce ta kai korafi ofishinsu
  • Bayan wanda ake zargin ya amsa laifinsa, Ismail Muhammed-Ahmed, alkalin kotun ya dage zaman zuwa ranar 27 ga watan Yuli don yanke hukunci

Kano - Wata kotun shari'ar Musulunci da ke zamanta a Kano, a ranar Alhamis ta bada umurnin a tsare wani Badamasi Abubakar a gidan gyaran hali bayan ya amsa laifin dage wa wata mata gyalenta ba da izininta ba.

Mr Abubakar, dan shekara 28, mazaunin Dan Marke Hotoro Quaters, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Za a shirya wasan kwaikwayo a kan tarihin tsige Sanusi I da Sanusi II a 1963 da 2020

Kotun Shariar Musulunci.
Kano: Kotun Musulunci Ta Ce A Bawa Abubakar Masauki a Gidan Yari Saboda Dage Wa Wata Gyale Ba Da Izininta Ba. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alkalin kotun, Ismail Muhammed-Ahmed, ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 27 ga watan Yuli don yanke hukunci.

Tunda farko, mai gabatar da kara, Sufeta Abdul Wada ya shaida wa kotun cewa wata Summaiya Abdul da ke zaune a Marke Hotoro Quarters, ta kai korafi a ofishin yan sanda da ke Hotoro a ranar 21 ga watan Yuni.

Mai gabatar da karar ya ce wanda ta yi karar ta yi ikirarin cewa misalin karfe 4 na yamma, wanda aka yi kararsa, ya dage mata gyale ba tare da izininta ba kuma da ta tunkare shi sai ya mare ta.

Mr Wada ya ce laifin ya ci karo da sashi na 165 da 166 na kundin Penal Code kamar yadda NAN ta rahoto.

A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa

Kara karanta wannan

Ba Zabin Biyan Tara: Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukuncin Dauri Saboda Satar Tukunyar Jar Miya Da Nama Zuku-Zuku A Ibadan

A wani labarin mai kama da wannan, Jami'an yan sanda na jihar Adamawa sun kama wani mutum mai shekaru 41, Usman Hammawa, bisa zarginsa da yi wa matarsa mai shekaru 36 duka, saboda N1,000 har sai da ta mutu.

Daily Trust ta ruwaito cewa rikici ya barke tsakanin Rabiyatu Usman da mijinta ne bayan ta bukaci ya biya ta bashin N1,000 da ya karba daga hannunta.

Usman Hammawa, mazaunin yankin Jada a karamar hukumar Ganye ta jihar Adamawa, ya halaka matarsa ne ta hanyar buga kanta da bango, hakan yasa ta fadi sumammiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel