Ba Mu Yarda Da Musulmi 2 Ba: Kungiya Ta Bayyana Kirista Da Ya Dace Tinubu Ya Dauka a Matsayin Mataimaki a 2023

Ba Mu Yarda Da Musulmi 2 Ba: Kungiya Ta Bayyana Kirista Da Ya Dace Tinubu Ya Dauka a Matsayin Mataimaki a 2023

  • Wata kungiyar matasan kudu da arewa ta yi Allah wadai da jita-jitar da ke yawo na cewa Bola Tinubu zai dauki musulmi a matsayin mataimakinsa a 2023
  • Kungiyar ta bakin shugabanta da sakatare ta yi gargadin hakan ba zai haifar da da mai ido ba, sannan ta bada shawarar a zabi SGF Boss Mustapha a matsayin mataimakin Tinubu
  • Matasan sun lissafa dalilai da dama da suka saka Barista Boss Mustapha ya fi kowanne mutum cancanta ya zama abokin takarar Bola Tinubu a zaben shekarar 2021

Kungiyar matasan Kudu da Arewa, 'The Southern-Northern Progressive Youth Congress' ta soki shirin da ake hasashen jam'iyyar APC na yi na zabarwa dan takararta, Asiwaju Bola Tinubu, wani musulmi a matsayin mataimaki a zaben 2023.

Kungiyar cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Nsebabi Brownson da Sakatarenta Bashir Aliyu Galadanci, sun goyi bayan a zabi Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Boss Mustapha a matsayin mataimakin Tinubu, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Kusoshi a Jam’iyya sun dage Tinubu ya dauki Mataimaki daga mutum 2 a Gwamnatin Buhari

Sakataren Gwamnatin Tarrayar Najeriya, Boss Mustapha.
Kungiya Ta Bayyana Kirista Da Ya Dace Tinubu Ya Dauka a Matsayin Mataimaki a Zaben 2023. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta ce:

"Mun yi Allah-wadai da jita-jitar cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Mai girma Asiwaju Ahmed Bola Tinubu zai dauki musulmi a matsayin mataimakinsa.
"Muna shawartar APC kada ta fada cikin tabon siyasa ta yarda a matsa mata lamba ta tsayar da musulmi da musulmi a zaben shugaban kasa na 2023 don kaucewa kallubalen da hakan ke iya haifar wa gwamnati mai zuwa.
"Kada mu manta abin da ya faru a babban zaben 1993 yadda takarar musulmi/musulmi na Alhaji M.K.O. Abiola da Alhaji Babagana Kingibe ya kare.
"Muna kira da babban murya a zabi Kirista a matsayin mataimakin Asiwaju Ahmed Bola Tinubu Jagaban na Borgu wanda ya ci zaben fidda gwani na APC."

Kungiyar ta bayyana dalilan da ya sa Boss Mustapha ya cancanci zama mataimakin Tinubu

Kara karanta wannan

Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto

Don haka, kungiyar ta bada shawarar a zabi SGF Mustapha, "saboda nagarta, kwarewa, biyayya ga tsare-tsaren jam'iyya, alfarma na siyasa idan an kwatanta shi da wasu da ta yiwu a zabe su mataimakin shugaban kasa.

"Duk duniya an sani cewa SGF Boss Mustapha mutum ne mai nagarta, abin dogaro kuma kwararren kirista daga arewa a gwamnati tare da alaka mai kyau a arewa da musulmi da kirista.
"Ayyukansa da halayensa sun janyo masa yabo daga mai gidansa, shugaban kasa, kuma yadda ya kula da annobar COVID-19 a Najeriya ya janyo masa farin jini a kasa da siyasa.
"Wannan da wasu abubuwan sune dalilan da yasa kungiyar ke kira ga APC da Jagaban na Borgu su zabi Barista Boss Mustapha don samun nasara mai sauki a 2023.
"Muna kira ga shugbannin APC a kasar su saurari muryar yan kasa su yi abin da ya dace.
"Muna bada shawara kuma muna fatan dan takarar shugaban APC, Ahmed Tinubu, Jagaban na Borgu, ya saurari yan Najeriya. Bishiya daya ba za ta zama jeji ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel