Abubuwa sun fara kankama, Peter Obi da Kwankwaso za su iya hada-kai a zaben 2023

Abubuwa sun fara kankama, Peter Obi da Kwankwaso za su iya hada-kai a zaben 2023

  • Akwai kokarin da ake yi na hada-kan ‘yan takaran jam’iyyun adawa na NNPP da na LP a zaben 2023
  • Peter Obi da Rabiu Kwankwaso za su yi takara a Labour Party (LP) da New Nigeria People’s Party (NNPP)
  • Kakakin LP ya nuna ana aiki da nufin jam’iyyun hamayyan su dunkule domin su iya karbar mulkin kasar

Abuja - Leadership ta rahoto cewa akwai kokarin da ake yi na hada kan jam’iyyun adawa na Labour Party (LP) da New Nigeria People’s Party (NNPP).

Mai magana da yawun kungiyar National Consultative Forum da jam’iyyar LP, Dr. Yunusa Tanko ya bayyana haka da aka yi magana da shi a gidan talabijin.

Da aka yi masa tambaya ko akwai maganar hada kan ‘dan takarar LP, Peter Obi da kuma Rabiu Kwankwaso na NNPP, sai ya nuna akwai yunkurin hakan.

Kara karanta wannan

Burin Atiku a zaben 2023: Ina sa ran 'yan Najeriya za su yi kasa-kasa da jam'iyyar APC

Dr. Yunusa Tanko ya ke cewa ba za a iya cewa an karkare magana ba, amma ana bakin kokari.

Kwankwaso da Obi za su hade?

Kamar yadda Tanko ya shaidawa manema labarai, an tado batun hada-kan NNPP da LP ne bayan la’akari da magoya bayan Rabiu Kwankwaso da na Peter Obi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa Obi ya yi karfi sosai a Kudancin Najeriya, don haka zai yi kyau ‘dan takaran ya hada-kai da wadanda suke da karfi sosai a yankin Arewacin kasar.

Sanata Kwankwaso
'Dan takaran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso a garin Kalaba Hoto: @SaifullahiMohHassan
Asali: Facebook

An rahoto Tanko yana cewa Obi da Kwankwaso sun nuna jajircewa da nagartarsu, kuma sun taimakawa marasa karfi a lokacin da suka samu madafan iko.

LP ta na neman goyon-baya

Dr. Tanko ya na fatan mutanen kasar nan za su marawa ‘yan takarar baya a zabe mai zuwa idan har hakarsu ta cin ma ruwa na tunkarar APC da PDP a tare.

Kara karanta wannan

Asirin ‘Yan ta’adda ya tonu, Dakarun Sojoji sun bankado shirin hare-haren da za a kai

Kakakin jam’iyyar ya kuma nuna babu wani rikicin cikin gida a LP kamar yadda ake rayawa.

A wani rahoton da jaridar Sun ta fitar, an ji Sakataren yada labaran NNPP na kasa, Dr. Agbo Major, yana cewa za a gwabza da ‘dan takararsu a zabe mai zuwa.

Agbo Major ya fadawa ‘yan jarida ta wayar salula cewa Rabiu Kwankwaso ba zai janye takararsa ba, kuma ba zai hada-kai da Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP ba.

Major yake cewa sam babu maganar zama da Atiku, sai dai ma wasu su shigo NNPP. Sakataren ya ce masu wannan maganar ba su san abin da suke fada ba.

Za ayi wa APC taron-dangi?

Rahoton da mu ka fitar a karshen makon da ya wuce ya nuna akwai yiwuwar Atiku Abubakar ya zauna da jam’iyyun NNPP da na LP domin ya hada-kai da su.

Jam’iyyar PDP ta na tsoron Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su kawo mata matsala a zaben shugaban kasa, hakan zai iya ba Bola Tinubu nasara a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel