Nan fa daya, Magoya bayan Bola Tinubu ba za su yarda da 'kulle-kullen' da ake yi a APC ba

Nan fa daya, Magoya bayan Bola Tinubu ba za su yarda da 'kulle-kullen' da ake yi a APC ba

  • Wasu daga cikin magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu sun ce ana kokarin zagaye gwaninsu a APC
  • Tinubu Support Organisation da Northern Young Professionals for Tinubu sun fito, sun yi magana
  • Kungiyoyin sun ce zaben fitar da gwani ya kamata a shirya, ba a tsaida ‘dan takara ta maslaha ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja – Wasu magoya bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun nuna rashin amincewarsu kan yunkurin da ake zargin wasu su ke yi a game da zaben 2023.

Daily Trust ta rahoto ‘yan Tinubu Support Organisation da Northern Young Professionals for Tinubu su na cewa ya kamata Bola Tinubu ya karbi mulki.

Wadannan kungiyoyi sam ba su yi na’am da ‘shirin’ da wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar APC suke yi na fito da ‘dan takarar shugaban kasa ta hanyar bin maslaha ba.

Kara karanta wannan

Gaskiyar magana: Jigo ya yi karin-kashe a kan sauya-shekar Tinubu daga APC zuwa SDP

Shugaban kungiyar NYPT na kasa, Abdullahi Tanko Yakasai, ya fito yana zargin cewa akwai wasu manyan APC da suke neman yi wa Tinubu taron dangi.

Magoya bayan tsohon gwamnan na Legas su na zo ne a shiga zaben fitar da gwani domin fito da wanda zai zama ‘dan takarar APC a zaben da za ayi a 2023.

Channels ta rahoto Abdullahi Tanko Yakasai yana cewa bai kamata jam’iyyar ta biyewa wasu daidaikun masu son zuciya su canza al’adar da aka saba ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu ya na tafi Hoto: Bola Tinubu
Asali: Facebook

“Mu na ganin kullin da wasu abokan gaban Bola Tinubu suke yi a jam’iyya domin kai uban gidanmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kasa.”
“Mu na so mu yi amfani da wannan dama, mu yi kira ga masu zaben ‘dan takara, musamman a Arewa, su zabi wanda zai iya kai mu ga nasara.”

Kara karanta wannan

Wasu Makusanta da Mukarraban Shugaban kasa 7 da suka gagara samun takara a APC

- Abdullahi Tanko Yakasai

Ja da Atiku sai Tinubu - Disciples of Jagaban

Shi ma shugaban tafiyar nan ta Disciples of Jagaban (DOJ), Abdulhakeem Alawuje ya ce Tinubu ne kadai wanda zai iya doke Atiku Abubakar da PDP ta tsaida.

Jaridar ta ce Abdulhakeem Alawuje ya ja-kunnen jagororin APC da ke kokarin kauda Tinubu da su sani cewa yin hakan tamkar tabo tsuliyar dodo ne a siyasa.

Kungiyar magoya bayan ta ce idan mutane nan suka yi nasarar hana Tinubu takara, za su yi nadama domin a karshe matsalar da za a shiga za ta taba kowa.

An kai Atiku gaban kotu kan 2023

A makon nan aka samu rahoto, wani Lauya mai suna Johnmary Jideobi ya je kotu a Abuja, ya shigar da kara a kan Atiku Abubakar, PDP da hukumar INEC.

Lauyan ya nemi Alkali ya hana jam’iyyar PDP tsaida Atiku Abubakar takara a duk wani zaben Najeriya, dalilinsa kuwa shi ne 'dan siyasar ba 'dan kasa ba ne.

Kara karanta wannan

2023: Allah ne ya turo Tinubu ya gyara Najeriya, inji fitaccen malamin addini

Asali: Legit.ng

Online view pixel