2023: Ɗan Takarar Gwamna a PDP Ya Buƙaci a Dawo Masa Da Kuɗinsa N21m Da Ya Lale Ya Siya Fom

2023: Ɗan Takarar Gwamna a PDP Ya Buƙaci a Dawo Masa Da Kuɗinsa N21m Da Ya Lale Ya Siya Fom

  • Ambasada Wilfred Bonse, ya janye batun takararsa na gwamna karkashin jam’iyyar PDP a Jihar Cross River, hakan ya sa ya nemi a biya shi kudin fom din takarar da ya siya N21m
  • A cewar Bonse, jam’iyyar ta ki tantance shi don ya yi takara ko kuma ta bayyana rashin cancantarsa yayin da za a yi zaben fidda gwani ranar Laraba
  • Kamar yadda wani jami’in jam’iyyar ya bayyana, ba a mayarwa kowa kudin siyan fom din takara don haka dakyar a mayar wa dan takarar kudinsa

Cross River - Wani dan takarar gwamna a Jihar Cross River karkashin jam’iyyar PDP a 2023, Amb. Wilfred Bonse ya nemi jam’iyyar ta dawo masa da kudin fom din takararsa Naira miliyan 21, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Dan takarar PDP ya kwato N100m daga hannun deleget ta hanyar amfani da mafarauta da ’yan banga

A wata tattaunawar da NAN ta yi da Bonse a ranar Talata, ya bayyana batun bukatar a mayar masa da kudin fom din takarar saboda yadda jam’iyyar ta ki tantance shi don ba shi damar shiga takarar zaben fidda gwanin gwamnoni na Jihar Cross River.

2023: Ɗan Takarar Gwamna a PDP Ya Buƙaci a Dawo Masa Da Kuɗinsa N21m Da Ya Lale Ya Siya Fom
2023: Ɗan Takarar Gwamna a PDP Ya Nemi a Dawo Masa Da Kuɗinsa N21m Da Ya Lale Ya Siya Fom. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani jami’in jam’iyyar ya ce in har mutum ya riga ya siya fom din takara, jam’iyya ba za ta taba mayar masa da kudinsa ba.

Bonse ya ce jam’iyyar ta ki nuna rashin cancantarsa ko kuma ta ba shi damar tsayawa don a yi zaben fidda gwanin ranar Laraba da shi.

Dalilinsa na bukatar kudin fom din

Ya kara da cewa:

“Ina bukatar jam’iyyar ta maido min da Naira Miliyan 21 na kudin fom din takarar da na siya. Misali da an ba ni damar shiga takara don yin zaben fidda gwani, da ban damu ba. Amma sai aka mayar da ni can gefe.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari bai aminta da deleget din jam’iyyar ba

“Wani mamban Kwamitn Amintattu (BOT) ya turawa PDP wasika ya na neman ta duba matsalata don kada jam’iyyar ta rasa kujerar gwamna a zaben da za ayi musamman ganin matsayina. Amma duk da haka sun rufe kunnuwansu yayin da lokaci ya ke kara kurewa.
“Sabuwar Dokar Zabe ta tanadar da tantance dan takara ana saura kwana bakwai zaben fidda gwani, kuma babu sunana a cikin wadanda aka turawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC).”

Ya ci gaba da cewa bai san menene matsalar ba, kila akwai wadanda ke adawa da tsayawarsa takara. Hakan ya sa su ke son hana shi yin zaben fidda gwani.

Ya ce zai sauya sheka don ya tsaya takara

Ya ci gaba da cewa Cross River ta fi karfin kowa kuma ta fi karfin ko wacce jam’iyya. Kuma zai nemi takara karkashin wata jam’iyyar ta daban.

Bonse ya bayyana yadda ya tura wasika da bukatarsa ga shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sen. Iyorchia Ayu, inda ya amsa kuma ya mika ta ga ofishin jam’iyyar na kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Shahararren Mawakin Najeriya ya yi nasarar samun takarar ‘Dan Majalisa a PDP

A wata takarda wacce NAN ta gani, ya ce ya janye batun takararsa ne daga jam’iyyar, saboda duk kokarin da ya yi na neman adalci a PDP bai yiwu ba, don sun hana shi shiga zaben fidda gwani.

Ya kuma bayyana batun sauya shekarsa daga PDP zuwa wata tare da daruruwan mabiyansa.

Ya ce har an fara tantance shi aka dakata

Wakilin NAN ya nemi sanin idan wani ya gayyace shi don tantance shi, inda ya ce eh.

Ya ce yayin da ake duba takardunsa, an nemi ya gabatar da takardun biyan harajinsa, katin zabensa da kuma takardar haihuwarsa da tabbacin kotu, wadanda duk a cewarsa ya gabatar.

Ya ci gaba da cewa kwamitin tantancewar ta nemi takardar shaidar hidimar kasarsa (NYSC) wacce ya bayyana cewa ya bukata daga wurin NYSC din kuma an tabbatar masa da cewa ana shirin fitar masa da ita da zarar sun fara.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin PDP: Gwamna ya yi nasara, wasu sanatoci masu ci sun sha kaye

“A nan ne su ka dakata, inda su ka mayar da ni sauna ba tare da sun ci gaba da tambayata komai ba,” a cewar Bonse.

Katsina Ba Ta Siyarwa Ba Ce, Ɗalibai Ga Wakilan Jam'iyyu

A wani rahoton, Kungiyar Hadin Kan Daliban Jihar Katsina ta shirya zanga-zangar lumana musamman ga wakilan manyan jam’iyyu akan su zabi ‘yan takarar gwamna na kwarai wadanda za su ciyar da jihar gaba.

Daily Trust ta ruwaito cewa daliban sun dinga zagaye manyan titinan da ke garin Katsina rike da takardu wadanda su ka rubuta, “Jihar Katsina ba ta siyarwa ba ce”.

Yayin zantawa da manema labarai, shugaban daliban, Aliyu Mamman, ya nemi wakilan su duba zabin da ke zuciyoyin mutanen jihar wadanda su ka zarce mutane miliyan takwas a zuciyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164