Zaben fidda gwanin PDP: Gwamna Ortom ya yi nasara, Sanatoci masu ci sun sha kaye

Zaben fidda gwanin PDP: Gwamna Ortom ya yi nasara, Sanatoci masu ci sun sha kaye

  • Gwamnan jihar Benue ya samu tikitin tsayawa takarar sanata a mazabarsa, ya magantu kan wannan yanayi
  • Ya ce ya godewa jama'arsa bisa ba shi damar sake mulkarsu, inda ya ce aikinsu ya sa a gaba idan ya ci zabe
  • A bangare guda, wasu sanatoci masu ci sun rasa kujerunsu na takara duk dai a zaben fidda gwanin na yau

Jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom ya lashe tikitin takarar jam'iyyar PDP na zaben 2023 a gundumar Benue ta Arewa maso Yamma.

Fitowar Ortom a zaben ya biyo bayan karbarsa da wakilai daga kananan hukumomi bakwai da suka hada da shiyyar Benue ta Arewa maso Yamma, Daily Trust ta ruwaito.

A watan Maris din bana ne masu ruwa da tsaki daga shiyyar suka amince da shi a matsayin dan takarar sanata na PDP daya tilo da zai tsaya takarar kujerar Sanata.

Kara karanta wannan

Zulum: Allah ke ba da mulki, ba zan roki wani ya dauke ni abokin takarar shugaban kasa ba

Gwamna Ortom ya samu tikitin zama sanata
Zaben fidda gwanin PDP: Ortom ya yi nasara, Sanatoci masu ci sun sha kaye | Hoto: learserhip.ng
Asali: Twitter

Gwamnan ya shaida wa manema labarai a Makurdi jim kadan bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, cewa yana jinjinawa jama’arsa da suke tare da shi a ko da yaushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya ji dadin sake ba shi damar sake neman yi wa jihar hidima a majalisar dattawa idan a karshe wa’adinsa na gwamna ya kare.

Don haka Ortom ya yi alkawarin ci gaba da yin iya bakin kokarinsa na yi wa al’ummar mazabarsa hidima domin ya ce amfanar jama’a zai sa a gaba.

Sanatoci sun sha kaye a zaben fidda gwani

A halin da ake ciki kuma, a jihar Ondo, Sanata mai wakiltar mazabar Ondo ta Kudu, Nicholas Tofowomo, ya fuskanci kaye a yunkurinsa na komawa zauren majalisar dattawa a dandalin PDP.

Ya rasa tikitin komawa majalisa, inda tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Hon Agboola Ajayi ya samu tikitin.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya bayyana irin yadda yake matukar son gaje Buhari, ya ce ba wasa yake ba

Ajayi ya samu kuri’u 78 inda ya doke Tofowomo wanda ya samu kuri’u 74, rahoton Daily Post.

Sanata mai wa’adi biyu, Ayo Akinyelure, mai wakiltar Ondo ta tsakiya, shi ma ya rasa kujerar sa zuwa hannun Ifedayo Adedipe.

Shugaba Buhari ga Najeriya: Ba zan huta ba har sai an samu zaman lafiya a kasar nan

A wani labarin, Channels Tv ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kokarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

Buhari ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin bikin cika shekaru 58 da kafa rundunar sojojin saman Najeriya a Kano, TheCable ta ruwaito.

Shugaban ya ce zuba jarin da gwamnatinsa ta yi a rundunar sojin sama ya taimaka wajen karya lagwon 'yan ta'adda a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel