2023: Shahararren Mawakin Najeriya ya yi nasarar samun takarar ‘Dan Majalisa a PDP

2023: Shahararren Mawakin Najeriya ya yi nasarar samun takarar ‘Dan Majalisa a PDP

  • Jam’iyyar PDP za ta tsaida Olubankole Wellington a matsayin ‘dan takararta a mazabar Eti-Osa
  • Olubankole Wellington watau Banky W zai gwabza da wanda APC ta ba tikiti a takarar ‘dan majalisa
  • Banky W ya yi suna wajen harkar waka da yin fim, ya shiga siyasa da nufin kawo sauyi a Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Fitaccen mawakin nan ‘dan kasar Najeriya da kuma Amurka, Olubankole Wellington, wanda aka fi sani da Banky W ya samu tikiti a PDP.

Vanguard ta kawo rahoto a ranar Litinin 23 ga watan Mayu 2022 da ya tabbatar da cewa Mista Olubankole Wellington zai yi takara a jam’iyyar PDP.

Banky W shi ne wanda ya lashe zaben fitar da gwani na kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Eti-Osa a jihar Legas da PDP ta gudanar.

A karshen makon da ya gabata ne jam’iyyar PDP ta shirya zabukan tsaida gwani domin fitar da wadanda za su yi mata takarar majalisa a zabe na 2023.

Mawakin yana cikin wadanda suka samu nasara a kan abokan hamayyarsu a jam’iyyar adawar.

2023: Shahararren Mawakin Najeriya ya yi nasarar samun takarar ‘Dan Majalisa a PDP
Tauraro Olubankole Wellington Hoto: @Banky W
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Premium Times ta ce Wellington ya ci kuri’a 28, don haka aka tabbatar da shi a matsayin wanda zai rikewa jam’iyyar hamayyar tuta a mazabar Eti-Osa.

Wannan ne karo na biyu

Idan za a tuna, Tauraron mawakin ya nemi wannan kujera a zaben 2019 a karkashin sabuwar jam’iyyar Modern Democratic Party da aka kafa a 2017.

Mista Wellington ya sha kashi ne a hannun ‘dan takaran da APC ta tsaida, Babajide Obanikoro.

Kwanakin baya sai mawakin ya bada sanarwar cewa ya fice daga jam’iyyar MDP, ya koma PDP da nufin takara a babbar jam’iyya a zaben shekarar badi.

Wanene Banky W?

Shekaru kimanin 40 da suka wuce aka haifi Olubankole Wellington a kasar Amurka. Wannan ya sa mawakin ya zama yana da shaidar zama 'Dan Amurka.

Bayan dawowarsa Najeriya ya fara wake-wake tun yana karami a coci. Daga baya Banky W ya gawurta, har ya zama yana cikin fitattun mawaka a yau.

Akwai masu takarar bogi a APC

Dazu aka ji labari Kayode Fayemi ya ziyarci jihar Neja da nufin samun kuri’un ‘yan APC a zaben fitar da gwani na takarar shugabancin Najeriya a 2023.

Tsohon Ministan ya yarda an gagara gyara wuta da inganta tsaro, ya sha alwashin zai magance matsalolin kasar, ya ce shi da gaske yake takara a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel