Tsohon Shugaban APC, Oshiomhole ya fallasa Gwamnan da ya roke shi ya murde zabe a 2020

Tsohon Shugaban APC, Oshiomhole ya fallasa Gwamnan da ya roke shi ya murde zabe a 2020

  • Adams Oshiomhole ya ce Gwamna Kayode Fayemi ya taba nemansa da ya murde wani zabe a APC
  • Dr. Fayemi ya karyata wannan zargin, ya ce bai taba tunkarar Oshiomhole da maganar magudi ba
  • Oshiomhole da Fayemi sun samu sabani ne a kan hana Godwin Obaseki tikitin tazarce a jihar Edo

Abuja - Mai girma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya karyata Adams Oshiomhole a kan zargin da ya jefe shi da shi na neman ya murde zabe.

Gwamna Kayode Fayemi ya musanya wannan zargi da Adams Oshiomhole ya yi a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin Channels a makon nan.

A hirar da aka yi da Oshiomhole, ya bada labarin yadda gwamnan na Ekiti ya bukaci ya yi amfani da karfinsa domin ya yi son kai a wajen bada takara.

Kara karanta wannan

Na karanta Kur’ani, babu inda aka ce a hallaka mai zagin Annabi – ‘Dan takaran Shugaban kasa

Adams Oshiomhole ya bayyana cewa hakan ya faru ne a lokacin da yake rike da jam’iyyar APC.

Abin da ya faru a lokacin

Shi dai Oshiomhole ya yi ikirarin Fayemi ya fada masa baki da baki cewa idan su na son ‘dan takara, dole ayi duk abin da za ayi domin ya samu tikiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar tsohon gwamnan, ya fadawa Fayemi ba zai yiwu ayi amfani da shi wajen zalunci ba, har ya fi sauki a tunbuke shi, da a same shi da murde zabe.

Tsohon Shugaban APC
Adams Oshiomhole da wasu 'yan APC a Aso Villa Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Ba gaskiya ba ne - Fayemi

Kamar yadda mu ka samu labari daga The Nation, Dr. Fayemi ya maidawa tsohon shugaban na APC raddi, ya ce har yanzu yana yi masa kallon abokinsa.

Amma duk da tarayyarsu a siyasa, Fayemi ya ce sun sha banbam da Oshiomhole a kan yadda aka hana Godwin Obaseki samun tikitin APC da karfi da yaji.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Bugu da kari, tsohon Ministan ya zargi Oshiomhole da karfa-karfa a lokacin yana shugabancin APC. A karshe dai aka tunbuke shugaban na APC a 2020.

Jawabin Gwamnan Ekiti

“Domin fitar da mutane daga shakku, Gwamna Fayemi bai da dalilin da zai tunkari Oshiomhole saboda neman alfarmar wani zabe.”
“Fayemi ya yi abin a zo-a gani wajen nuna ya yarda da tsarin damukaradiyya a duk runtsi.”

- Gwamnatin jihar Ekiti

ICIR Nigeria ta ce shugaban kungiyar gwamnonin kasar ya kalubalanci tsohon gwamnan na Edo ya kawo hujjar da za ta gaskata abin da ya fadawa Duniya.

APC za ta hana Kudu takara?

Kwanaki kun ji labari cewa babu mamaki jam’iyyar APC ta canza shawara, ta tsaida ‘Dan Arewa a matsayin wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a 2023

Idan haka ba ta yiwu ba, za a iya dauko Musulmi da Musulmi domin a hana jam'iyyar PDP tattara kuri’un da za su fito daga Arewacin Najeriya a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Sarkin Bauchi ya yi maza ya yi karin-haske, ya karyata jita-jitar goyon bayan Osinbajo

Asali: Legit.ng

Online view pixel