Na karanta Kur’ani, babu inda aka ce a hallaka mai zagin Annabi – ‘Dan takaran Shugaban kasa

Na karanta Kur’ani, babu inda aka ce a hallaka mai zagin Annabi – ‘Dan takaran Shugaban kasa

  • Fasto Tunde Bakare ya yi Allah-wadai da yadda wasu Bayin Allah suka hallaka Deborah Samuel
  • Faston ya ce a musulunci aka haife shi, kuma bai taba ganin inda Al-Kur’ani ya yi umarni da haka ba
  • Tunde Bakare yana neman takarar shugaban kasa, shi ne limamin cocin Citadel Global Community

Abuja - Shugaban katafaren cocin na Citadel Global Community Church, Fasto Tunde Bakare ya yi Allah-wadai da kisan Deborah Samuel da aka yi a Sokoto.

Punch ta ce Fasto Tunde Bakare ya fitar da jawabi na musamman a game da wannan lamarin.

Deborah Samuel ta gamu da ajalinta ne bayan ta zagi Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW). Wannan abin dai ya faru ne a kwalejin ilmi na Shehu Shagari.

Da yake bayani a jawabin na sa, mai neman kujerar shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC ya ce kisan wannan Budurwa ya sabawa koyarwar musulunci.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

Tunde Bakare ya ce babu inda Al-Kur’ani ya yi umarni da a hallaka wanda ya zagi Annabi SAW.

Jaridar Daily Post ta ce shahararren Faston ya yi kira ga al’umma da su hada-kansu, sannan a rika ganin darajar Bil Adama, ya ce bai dace a hallaka rai ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fasto Tunde Bakare
Tunde Bakare a fadar Shugaban kasa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Ina mai matukar takaici da samun labarin mummunan kisan da aka yi wa Deborah Samuel a kwalejin ilmi na Shehu Shagari da ke garin Sokoto.”
“Babu wani ‘Dan Najeriya ko ma Bil Adama da ya cacanci mutuwa ta irin wannan yanayi na rashin tausayi a hannun ‘yan uwansa ‘Yan Adam.”
“A matsayin ‘yan kasa daya masu bambancin mutane da al’adu, akwai hanyoyin magance sabani, ko me ya faru, bai dace a dauki doka ba."

Ba haka Musulunci ya koyar ba

“A matsayina na wanda ya taba zama rikakken Musulmi, kuma wanda ya karanta Kur’ani daga shafin farko zuwa na karshe, babu inda aka yi umarni da abin da aka yi wa Deborah Samuel.”

Kara karanta wannan

Deborah Samuel: Ƴan Najeriya Sun Yi Wa Ɗan Tsohon IGP Martani Kan Kalamansa Game Da Kisar Ɗalibar Sokoto Da Ta Zagi Annabi

Faston ya ce Musulunci addini ne mai son zaman lafiya, har ya bayyana cewa kakansa shi ne babban limamin masallacin Iporo Sodeke a garin Abeaokuta.

Pulse ta ce Bakare ya bada labarin yadda mahaifinsa ya zauna a kauyen Shagari a lokacin ana noman auduga, sai ga shi yau ana neman kawo rikicin addini.

A karshe Bakare ya aika ta’aziyyarsa ga ‘yan uwan Marigayiyar a kan wannan rashi da suka yi.

Ra'ayin Ahmad Gumi

A game da wannan lamari na batanci, an rahoto Sheikh Ahmed Gumi, ya na cewa wadanda ba musulmi ba sun zagi Annabi Muhammad (SAW) da yake raye.

Shehin malamin ya ce duk da cin mutuncinsa da aka yi a wancan lokaci, Manzon Allah (SAW) bai taba kowa ba, balle har a je ga ya kashe masu ci masa zarafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel