2023: Bafarawa da wasu mutum 4 da su ka hakura da neman Shugaban kasa da dalilansu

2023: Bafarawa da wasu mutum 4 da su ka hakura da neman Shugaban kasa da dalilansu

  • Wasu daga cikin wadanda aka yi tunanin za su yi takarar shugaban kasa a zaben 2023 sun janye
  • Adamu Garba wanda ya yi niyyar neman tikiti a APC shi ne na karshe a jerin wadanda suka hakura
  • Kafin nan, Attahiru Dalhatu Bafarawa da Dr. Doyin Okupe sun fasa neman takara a zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta kawo maku jerin fitattun ‘yan siyasan da suka ba magoya bayansu kunya, su ka fasa fitowa neman takarar kujerar shugabancin Najeriya.

Ga cikakken jerin nan:

1. Adamu Garba (Rashin kudi)

Bayan ya ayyana shirin takara da neman gudumuwa saboda shiga zaben 2023, sai aka ji Adamu Garba, ya ajiye wannan maganar saboda tsadar kudin fam.

Da yake magana a Facebook, Garba ya bayyana cewa ya tattauna da masu taya shi yakin neman zabe, ya amince ya janye takarar duk da an tara masa N83.2m.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

2. Doyin Okupe (Lokacin Ibo ne)

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin magana tayi nisa aka rahoto Dr. Doyin Okupe yana cewa ya janye kansa daga cikin wadanda za su nemi kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Tsohon hadimin shugaban Najeriyan ya koma goyon bayan yankin Ibo, ya kuma yi kira ga sauran masu harin zuwa Aso Villa su marawa Peter Obi baya a PDP.

Bafarawa da wasu mutum 2
Okupe, Bafarawa da Garba II Hoto: Adamu Garba II, Farfajiyar-matasan-arewa, da www.pulse.ng
Asali: UGC

3. Moses Ayom (An hana Arewa tikiti)

Kwanakin baya Moses Ayom ya shaidawa Duniya ba zai nemi tikitin takarar shugaban kasa a APC ba. Dalilinsa shi ne an ki ware tikiti zuwa ga yankin da ya fito.

Ayom ya sallamawa majalisar NWC na APC da ta ke karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu a yau, wanda ya fito daga bangaren Arewa maso tsakiya.

4. Attahiru Bafarawa (Tsufa ya zo)

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

A wata hira da aka yi da shi, tsohon gwamnan Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana cewa ba zai sake neman wata kujera ko mukamin siyasa a Najeriya ba.

Attahiru Bafarawa kwararren ‘dan siyasa ne wanda ya nemi takarar shugaban kasa tun a 2007. A 2023, Bafarawa ba zai roki kuri’un jama’a a kowace jam’iyya ba.

5. Orji Uzor Kalu (Rashin ware tikiti)

A ranar Talata aka ji Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu ya ce ba zai fito neman tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023 ba.

Uzor Kalu ya ajiye batun takarar shugaban kasa a gefe, ya ce zai nemi ya koma majalisa. Tsohon Gwamnan ya koma marawa takarar Sanata Ahmad Lawan baya.

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel