Shugaban kasa a 2023: Aminu Tambuwal ya nuna karfin gwiwar mallakar tikitin PDP

Shugaban kasa a 2023: Aminu Tambuwal ya nuna karfin gwiwar mallakar tikitin PDP

  • Gwamna Aminu Tambuwal ya nuna karfin gwiwar samun nasara a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP
  • Tambuwal wanda ya kasance daya daga cikin manyan masu neman darewa kujerar Buhari a babbar jam’iyyar adawar kasar, ya ce nasararsa tabbatacciya ce
  • Gwamnan na Sokoto na daya daga cikin yan takarar jam’iyyar masu jini a jika kuma shine shugaban kungiyar gwamnonin PDP

Kaduna - Yayin da yan siyasa ke gwagwarmayar mallakar tikitin takarar shugaban kasa a karkashin inuwar People’s Democratic Party (PDP), Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya nuna karfin gwiwar yin nasara a zaben fidda gwanin jam'iyyar mai zuwa.

Tambuwal ya bayar da tabbacin ne jim kadan bayan ya kada kuri’arsa a taron jam’iyyar PDP na shiyyar arewa maso yamma wanda aka yi a jihar Kaduna, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Ya ce gudanar da taron jam’iyyar na yankin da aka yi cikin nasara alama ce da ke nuna cewa taronta na kasa zai gudana cikin lumana da nasara a bangarensa.

Shugaban kasa a 2023: Aminu Tambuwal ya nuna karfin gwiwar mallakar tikitin PDP
Shugaban kasa a 2023: Aminu Tambuwal ya nuna karfin gwiwar mallakar tikitin PDP Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Ya yi bayanin cewa:

“Kun san arewa maso yamma na taka muhimmiyar rawar gani a siyasar Najeriya da tsarin siyasar Najeriya, na yi imanin hakan wata alama ce gabannin babban taron na kasa cewa za mu kai wajen da yardar Allah, mu shirya sannan mu yi taro mai cike da nasara.”

Da rakiyar abokansa na siyasa, tsohon kakakin majalisar wakilan ya kada kuri'arsa jim kadan bayan tantance shi daga cikin hakokin jam'iyyar.

Ya kuma yabawa shuwagabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki bisa irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen gudanar da taron cikin nasara.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP sun shirya ganawar gaggawa gabanin zaben fidda gwani

Rahoton ya nakalto Tambuwal na cewa:

“Mun gode ma Allah cewa taron jam’iyyarmu ta PDP a yankin arewa maso yamma da aka dage ya gudana cikin nasara ba tare da matsala ba; muna godiya ga dukkanin shugabannin jam’iyyar daga yankin arewa maso yamma da wakilan da suka halarci taron.
"Muna godiya ga kowa da kowa har ma da jami'an tsaro saboda rawar da suka taka wajen tabbatar da cewa mun yi taro cikin nasara."

Sauran manyan yan siyasa da suka halarci taron sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ahmed Mohammed Makarfi.

Sauran sune tsohon mataimakin gwamnan Sokoto kuma tsohon ministan albarkatun ruwa, Muktar Shagari da tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahadi Ali da sauransu.

Fom din takara N100m: NNPP za ta ba ku mamaki a zaben 2023, Kwankwaso ya yi kaca-kaca da APC

Kara karanta wannan

Wani dan takarar shugaban kasa ya karaya ya kai karar PDP kan kudin fom N40m

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya caccaki jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan siyar da fom dinta na shugaban kasa a kan naira miliyan 100, yana mai cewa fom din jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) bai da tsada.

Kwankwaso wanda ya yi magana a taron shugannin NNPP na farko a Abuja, ya bayyana cewa jam’iyyarsu ba irin APC bace wacce ta tsawwala kudin fom dinta na shugaban kasa har naira miliyan 100, jaridar Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel