Mai neman Shugaban kasa a APC ya hakura, Kalu ya fadi wanda yake marawa baya a 2023

Mai neman Shugaban kasa a APC ya hakura, Kalu ya fadi wanda yake marawa baya a 2023

  • Orji Uzor Kalu ya ce ba zai fito neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC a zabe mai zuwa ba
  • Sanata OrjiUzor Kalu ya ajiye batun takarar a gefe guda ne tun da an ki yarda a ba yankin Ibo tikiti
  • Tsohon Gwamnan na jihar Abia zai yi takarar Sanata, kuma yana goyon bayan Ahmad Lawan a 2023

Abuja - Shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya, Orji Uzor Kalu ya yanki fam domin takarar kujerar Sanata a yankin jihar Abia ta Arewa.

Daily Trust ta ce Sanata Orji Uzor Kalu ya shaidawa Duniya wannan ne a wani jawabi na musamman da ya saki a ranar Litinin, 10 ga watan Mayu 2022.

‘Dan siyasar yana cikin wadanda suka fito da farko su na cewa za su yi takarar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

Dalilin Orji Uzor Kalu na fasa neman mulkin Najeriya shi ne manyan jam’iyyu na APC da PDP sun ki kai takararsu zuwa yankin da ya fito na Kudu maso gabas.

Zan sake neman Sanata - Kalu

Tun da an bar kofa a bude ga duk mai sha’awa ya tsaya takarar shugaban kasa, Kalu ya ce ya zabi ya koma majalisa domin cigaba da aikin alherin da yake yi.

“Na kuma yanki fam domin takarar Sanata mai wakiltar mazabar Abia ta Arewa domin karasa aikin alherin da na fara yi wa Arewacin Abia.”

- Orji Uzor Kalu

Mai neman Shugaban kasa a APC
Sanatan APC, Orji Uzor Kalu a ofishinsa Hoto: @orji.kalu.79
Asali: Facebook

The Nation ta ce an ji tsohon gwamnan yana nuna goyon bayansa ga Sanata Ahmad Lawan a APC.

Uzor Kalu yana tare da Lawan

“Ina taya abokina, tsohon abokin zaman daki na kuma mai gidana, Ahmad Lawan murna da ya yanki fam din takarar shugaban Najeriya a jam’iyyarmu.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

“Na ji matukar dadi da ya yi, domin ya fito ne daga Arewa maso gabas, yankin da kamar na Kudu maso gabas, bai taba fito da shugaban Najeriya ba.”
“Na dade ina kira ga adalci da gaskiya a kasarmu, ina cewa shugaban da za ayi bayan Muhammadu Buhari ya zo daga Arewa ta gabas ko Kudu ta gabas.”

- Orji Uzor Kalu

Kalu ya ce tun da ba za a samu ‘dan yankinsa da zai yi takara ba, zai bada cikakkiyar goyon bayansa ga shugaban majalisar dattawa a zaben da za ayi a 2023.

‘Dan majalisar ya yi kira ga aminansa, abokansa a siyasa da sauran ‘Yan APC su marawa Lawan baya.

Takarar Jonathan a APC

Jim kadan bayan an yi masa tayin neman takara a APC, sai aka ji labari cewa Dr. Goodluck Jonathan yana gidan shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.

An fahimci Goodluck Jonathan ya nemi ya sake takarar shugaban kasa, amma wasu makusantansa su ka ba shi shawara, sai ya hakura da wannan maganar.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel