2023: Jerin yan takarar shugaban kasa na APC 23 da yankin da suka fito
Gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, mambobin jam’iyyar da dama sun ayyana kudirinsu na son darewa babbar kujerar siyasar kasar.
Adadin wadanda ke son gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari na karuwa a kullun, lamarin da yasa jam’iyyar ta kara wa’adin siyar da fom dinta na takara wanda farashinsa yake kan naira miliyan 100.
Zuwa yanzu, wasu yan takara sun rigada sun siya fom dinsu.
Ga jerin wadanda suka ayyana kudirinsu na son mallakar tikitin shugaban kasa na APC:
Kudu maso Yamma
1. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP
2. Fasto Tunde Bakare
3. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
4. Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti
5. Tsohon kakakin majalisar wakilai Dimeji Bankole
6. Mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ajayi Boroffice
7. Sanata Ibikunle Amosun
Kudu maso Gabas
1. Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi
2. Sanata Orji Uzor Kalu
3. Sanata Rochas Okorocha
4. Ministan kwadago Chris Ngige
5. Karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba
6. Tsohon shugaban majalisar dattawa Ken Nnamani
7. Ministan kimiyya da fasaha Ogbonnaya Onu
8. Uju Ohanenye (mace)
Kudu maso Kudu
1. Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River
2. Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole
3. Ministan harkokin Neja Delta Godswill Akpabio
4. Fasto Nicholas Felix
5. Ministan sufuri Rotimi Amaechi
Arewa ta tsakiya
1. Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi
Arewa maso yamma
1. Toshon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Yerima
2. Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa
Asali: Legit.ng