Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

  • Kallo ya koma sama baki ya ƙi rufuwa yayin da Sanata Kwankwaso ya dira Kano daga Abuja tare da jiga-jigan APC mai mulki
  • Tsohon hadimin Buhari, Kawu Sumaila, Albdulmumini Jibrin, suna cikin tawagar da ta dira Filin Malam Aminu Kano tare da Kwankwaso
  • Wata majiya tace Shekarau ya kammal shirin sauya sheƙa zuwa NNPP kuma zai sanar gobe Asabar

Kano - Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya dira cikin birnin Kano tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC da ke shirin sauya sheka zuwa NNPP.

Jagoran jam'iyyar NNPP mai kayan maramari na ƙasa, Kwankwaso ya dira Filin sauka da tashin jirgaen sama na Malam Aminu Kano da yammacin Jumu'a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Isar Kwankwaso Kano.
Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano Hoto: NNPP worldwide Platform/facebook
Asali: Facebook

Daga cikin fitattun yan siyasa da suka dira Kano tare da Kwankwaso akwai, tsohon kakakin majalisar dokokin jiha, Alhassan Rurum, daraktan Kanfen ɗin Tinubu, Abdulmumin Jibrin Kofa.

Sauran sune, ɗan majalisar wakilan taraya mai wakiltar mazaɓar Tofa/Dawakin Tofa/Rimingado, Abdulkadir Jobe, da tsohon hadimin shugaban ƙasa Buhari, Kawu Sumaila.

Dukkan waɗan nan jiga-jigan siyasa sun fice daga jam'iyyar APC a baya-bayan nan kuma ana tsammanin zasu sanar da shiga NNPP a hukumance a wurin wani taro da ke gudana yanzu haka a Kwankwasiyya House.

Meyasa babu Shekarau a ciki?

Wanda akai tsammani kuma ba shi a cikin wannan fita shi ne tsohon gwamna, Malam Ibrahim Shekarau, ana tsammanin zai diro tare da tawagarsa kuma ya sanar da sauya sheƙa zuwa NNPP.

Wani rahoton jaridar ya nuna cewa Shekarau ya dawo daga Abuja tun farko kuma be shiga cikin wannan tafiyar ba saboda tattaunawar neman shawari da yake cigaba da yi da makusantansa.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP

Amma wata majiya ta ce Shekarau ya kammala duk wasu shirye-shirye na sauya sheƙa daga APC zuwa NNPP kuma.zai sanar da haka ranar Asabar.

Legit.ng Hausa ta tuntuɓi wani ɗan Kwankwasiyya a Kano, Saidu Abdu, ya bayyana cewa tun kafin saukar Jirgin babu masaka tsinke, mutane ta ko ina.

Said Abdu ya shaida wa wakilan mu cewa:

"Tun daga saukar jagora Kwankwaso har zuwa gida mutane ta ko ina, haka muka raka shi da kyar na iya shiga gidan."
"Bayan an natsu shugaban jam'iyya ya sanar mana cewa gobe za'a je mazaɓar tsohon kakakin Majalisar jiha dake Rano a ba shi katin zama mamba, daga nan a wuce Sumaila a baiwa Kawu Sumaila katin zama ɗan jam'iyya.

Ɗan Kwankwasiyyan ya kara da cewa lokaci ya yi da jam'iyyar NNPP zata kwace mulkin Kano da kuma Najeriya baki ɗaya da ikon Allah.

A wani labarin kuma Buhari ya yi Allah wadai da kashe ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto, ya nemi a yi bincike

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi Alla wadai da rikicin da ya jawo kisan ɗalibar da ake zargi da ɓatanci a Sokoto.

Buhari ya ce musulman duniya na girmama dukkan Annabawan Allah, amma ba kyau ɗaukar doka a hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel