Idan Magajin Buhari ya fito daga Kudu sai ‘Yan Arewa sun fi morewa inji Sanatan Borno

Idan Magajin Buhari ya fito daga Kudu sai ‘Yan Arewa sun fi morewa inji Sanatan Borno

  • Mohammed Ali Ndume ya na tare da masu cewa a bar mutanen kudu su karbi ragamar shugabanci
  • Sanatan na kudancin jihar Borno ya ce mutanen Arewa za su fi amfana idan mulki ya bar hannunsu
  • A ra’ayin ‘dan siyasar, yankin kudancin Najeriya sun fi kowa morar gwamnatin Muhammadu Buhari

Abuja - Mohammed Ali Ndume, Sanata mai wakiltar kudancin Borno a majalisar dattawa, ya ce Arewa za ta fi amfana idan har mulki ya koma kudu.

Jaridar The Cable ta rahoto Sanata Mohammed Ali Ndume yana wannan magana a lokacin da ya yi hira da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

‘Dan majalisar ya bayyana cewa adalci da gaskiya shi ne wanda zai karbi mulki daga hannun Muhammadu Buhari a 2023 ya zama mutumin Kudu.

Kara karanta wannan

2023: Igbo Ba Abin Yarda Bane, Ba Mu Amince Su Mulki Ƙasa Ba, Ƙungiyoyin Arewa

A cewar Sanata, yankin Arewa ya fi amfana da gwamnatin tarayya sa’ilin da shugaba Goodluck Jonathan yake rike da kasar, duk da daga kudu ya fito.

Haka zalika Ali Ndume ya yi ikirarin bangaren Kudu su ka fi cin moriyar gwamnatin Buhari.

Ra'ayin da Ndume yake da shi

“Ni a karon kai na, ina jin zai fi yi mana kyau a samu shugaba daga Kudu. Shugaban yanzu ‘dan Arewa ne, amma idan ka lura da kyau, Kudu sun fi amfana.”
Sanatan APC
Sanatan Borno, Mohammed Ali Ndume Hoto: newswirengr.com

“Idan (bangaren Arewacin Najeriya) mu ka samu shugaban kasar Najeriya ‘dan Kudu, za mu fi amfana, kamar yadda aka yi a gwamnatin Jonathan.”
“Da Buhari ya hau mulki, Kudu sun fi amfana. Su ke da mataimakin shugaban kasa, kuma ya na da karfi domin Shugaba Buhari ya taba damka masa mulki."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Ribar da 'Yan kudu su ka samu

An rahoto Ndume ya ce mataimakin shugaban kasa da shugaban majalisar wakilai duk sun fito ne daga kudu maso yamma, baya ga manyan Ministoci.

Ministar kudi (kafin ta ajiye aikinta saboda badakalar NYSC), Ministan ayyuka, kiwon lafiya, harkar man fetur (karamin Minista), duk mutanen kudu ne.

A fannin samar da abubuwan more rayuwa, Sanatan ya ce Kudu sun samu gadar Neja, titin East-West, jirgin Legas-Ibadan, titin Legas-Ibadan da sauransu.

Ganin yadda abubuwa su ke tafiya, Ndume ya ke mara baya ga masu cewa mulki ya bar Arewa.

Za a ba 'Dan Arewa takara?

Ndume ya yi wannan magana ne ganin cewa ana labarin zai yiwu Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya nemi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.

Watakila yau Dr. Ahmad Lawan ya yanki fam na shiga zaben fitar da gwani a 2023. Hakan zai sa ya zama mutum na biyu da ke neman tikitin APC daga Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel