Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya bayyana alherin da ya shirya yiwa 'yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa
  • Saraki ya ce idan aka zabe shi zai tabbatar da gina gidaje 500,000 duk shekara ga 'yan Najeriya a mulkinsa
  • Ya kuma bayyana cewa, zai zama mai hada kan 'yan Najeriya; Kudu da Arewa, Musulmi da Kirista baki daya

Abuja - A ranar Alhamis ne tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya yi alkawarin gina gidaje 500,000 a duk shekara idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasan Najeriya a zaben 2023.

Saraki wanda ke tseren takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP ya kuma yi alkawarin zai zama gada tsakanin Arewa da Kudu da Kirista da Musulmi, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

Aniyar da Bukola Saraki ya daura ga Najeriya idan ya gaji Buhari
2023: Zan gina gidaje 500,000 duk shekara idan aka zabe ni, inji Saraki | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Saraki ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja.

“Zan gina gidaje 500,000 masu araha duk shekara. Zan kirkiro dandali mai inganci don kare nahiyar Afirka. Zan zama shugaban kasa ga kowa da kowa saboda zan wakilci Najeriya ne. Zan zama gada tsakanin Arewa da Kudu, Musulmi da Kirista.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, Bukola Saraki, ya ce zai kare kowane bangare na kasar nan daga ‘yan ta’adda da ‘yan fashi idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya ce dogaro da man fetur da al’ummar kasar ke yi zai zo karshe a mulkinsa saboda bangaren da ba na mai ba zai fi kawo ci gaba.

Yajin aikin ASUU: Daliban jami'a sun fusata, sun ba lakcarori da gwamnati wa'adi su bude jami'o'i

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

A wani labarin, kungiyar dalibai ta kasa (NANS) reshen kudu maso gabas ta baiwa gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) wa’adin kwanaki tara su bude dukkan jami’o’in gwamnati.

Ko’odinetan shiyyar NANS ta Kudu maso Gabas, Mista Moses Onyia, ya ba da wa’adin ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Lillian Orji, ya fitar a madadinsa, a ranar Talata a Enugu.

ASUU, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, ta tsawaita yajin aikin gargadi na watanni uku da karin wasu watanni ukun, wanda ta shiga tun a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel