2023: Igbo Ba Abin Yarda Bane, Ba Mu Amince Su Mulki Ƙasa Ba, Ƙungiyoyin Arewa

2023: Igbo Ba Abin Yarda Bane, Ba Mu Amince Su Mulki Ƙasa Ba, Ƙungiyoyin Arewa

  • Wasu kungiyoyin arewa sun ce bai dace a mayar da mulkin Najeriya hannun mutanen yankin Kudu maso Gabas ba idan zaben 2023 ya zo
  • Kamar yadda kungiyoyin su ka bayyana, ‘yan siyasar kudu ba abin amincewa ba ne musamman ganin furucin su na kwanan nan
  • Kungiyoyin sun kara da caccakar shugabannin yankin kudu maso gabas akan dagewarsu kan cewa lallai sai mulki ya koma yankinsu

FCT, Abuja - Hadin kan Kungiyoyin Arewa (CNGs) a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu ta nuna rashin jindadinta akan yadda Kungiyoyin Ibo da mutanen yankin kudu maso gabas su ka tashi hankalin Najeriya akan zaben shugaban kasa na 2023, Vanguard ta rahoto.

Kakakin CNGs, Abdulazeez Suleiman, ne bayyana wa manema labarai hakan, wanda wakilin Legit.ng ya halarci taron a Abuja, inda ya ce bai dace a amince wa Ibo su hau karagar mulki ba.

Kara karanta wannan

Igbo bai da amana, bamu yarda a ba su shugabancin kasa ba: Kungiyoyin Arewa CNG

2023: Igbo Ba Abin Yarda Bane, Ba Mu Amince Su Mulki Ƙasa Ba, Ƙungiyoyin Arewa
2023: Kungiyoyin arewa sun ce yan siyasa irin su Umahi ba abin yarda bane. Hoto: @EbonyiGov.
Asali: Twitter

Ya kara da cewa shugabannin Ibo sun yi barazana kwarai akan tsaron kasar nan inda su ka ja kunne cewa za su tayar da hankalin kasa idan ba a ba dan yankin kudu maso gabas damar gadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba.

Ya kuma caccaki shugabannin Ibo akan kiran da su ka dinga yi na sakin shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu.

Kamar yadda ya ce:

“Hadin kan Kungiyoyin Arewa ta yi nazari akan abubuwan da ke ta faruwa a Najeriya, musamman cikin ‘yan watanni kadan da su ka gabata lokacin da demokradiyya, hadin kan siyasa da kuma tsaron kasa su ka samu cikas, wanda aka ‘yan kabilar Ibo ne su ka dinga tayar da tarzomar.
“Wannan tabbataccen abu ne cewa shugabannin Ibo kamar tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma shugaban Kungiyar Tuntubar Shugabannin Ibo, Chukwuemeka Ezeife a lokacin sun kalubalanci ci gaba da dunkulewar Najeriya yayin da shugabanni Ibo su ka je yi masa ta’aziyya a ranar 5 ga watan Afirilun 2022.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

“Sannan shugabannin Ibo sun tayar da hankula duk don su samu a saki Nnamdi Kanu, shugaban IPOB wanda gwamnati ke ta shari’a da shi.”

Ya ci gaba da tunatar da yadda shugabannin Ibo su ka yi barazanar kawo cikas ga tsaro a ranar 4 ga watan Mayun 2022, idan har aka ki bai wa yankinsu damar shugabancin kasa a 2023.

Ya ce sun yi barazanar tayar da hankali, rikici da kuma rushe zaman lafiyan kasar nan.

A cewarsa wannan shi ne abu ma fi ban tsoro da zai sa a guji barin dan kabilar Ibo ya shugabanci kasar nan.

IPOB ta musanta batun kai farmaki ga ‘yan arewa mazauna yankin Kudu maso Gabas

Sai dai shugabancin IPOB ta musanta batun kai farmaki ga wani dan arewa ko kuma wanda ba dan Biafra ba da ke kasar Ibo.

Kamar yadda kungiyar ta nuna, ‘yan kabilar Ibo su na da matukar son jama’a da karamci kuma ba za su iya kai wa wani farmaki ba, hasali ma sai dai ba shi kariya.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Shugaban kasa ya tona asirin masu karyar sayen fam a jam’iyyar APC

Kakakin IPOB, Emma Powerful, ya bayyana hakan ta wata takarda wacce Legit.ng ta gani a ranar 12 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel