Shugabanci a 2023: Shehu Sani ya bayyana hanya daya da za ta sa dan Kudu ya gaji Buhari

Shugabanci a 2023: Shehu Sani ya bayyana hanya daya da za ta sa dan Kudu ya gaji Buhari

  • Sanata Shehu Sani ya yi duba ga batutuwan neman takarar shugaban kasa daga Kudancin kasar nan gabanin zaben 2023 mai zuwa
  • Tsohon dan majalisar kuma jigo a jam’iyyar PDP ya ce mulki zai koma Kudu ne kawai bayan saukar Buhari idan APC da jam’iyyarsa ta PDP suka mika tikitin zuwa yankin
  • Yayin da zabukan 2023 ke kara gabatowa, babu abu karara da ke nuna cewa manyan jam’iyyun biyu za su mika tikitin takarar shugaban kasa ga Kudancin kasar

Gabanin zaben 2023, Sanata Shehu Sani ya ce yiwuwar shugabancin kasar nan ya koma kudu ya ta'allaka ne da shawarin manyan jam’iyyu biyu (APC da PDP) su fito da 'yan takara daga yankin.

Sani, tsohon dan majalisar tarayya kuma jigo a jam’iyyar PDP daga jihar Kaduna, ya bayyana haka a wani sako da Legit.ng ta gani a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 3 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Ya rubuta:

“Mulki zai koma Kudu ne kawai idan aka zabo ‘yan takaran manyan jam’iyyun siyasa biyu daga Kudu”.

Peter Obi: Ya Zama Dole a Bar Kudu Maso Gabas Ta Mulki Najeriya a 2023

A baya kuwa, Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na PDP kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ce dole ne a ba dan yankin kudu maso gabashin kasar nan mulkinta, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya tsaya akan cewa zaben shugaban kasa dan kabilar Ibo ne kadai adalci da kuma nuna girma ga yankin don haka wajibi ne a ba su dama.

Obi ya yi wannan maganar ne a ranar Litinin yayin wani taro da wakilan jam’iyyar na Jihar Ogun da sauran shugabannin jam’iyyar PDP a ofishinta da ke Abeokuta, Jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Tsohon gwamnan ya bukaci wakilan da su kasance masu duba gaskiya, kada kudi ko son kai ya rinjaye su. A cewarsa, yana nan akan bakarsa na burin daukaka Najeriya ta yadda duk wani dan kasar zai yi alfahari da ita.

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.

Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta fallasa 'dabarar' da ta sa Jam’iyyar APC ta saida fam a kan N100m

Asali: Legit.ng

Online view pixel