Zaben 2023: PDP ta fallasa 'dabarar' da ta sa Jam’iyyar APC ta saida fam a kan N100m

Zaben 2023: PDP ta fallasa 'dabarar' da ta sa Jam’iyyar APC ta saida fam a kan N100m

  • Sakataren yada labaran PDP na kasa ya fitar da jawabi, yana zargin Gwamnatin APC da taba asusu
  • Debo Ologunagba ya ce APC ta tsula kudin fam ne saboda ta iya tara kudin da za ta shiga zaben 2023
  • Jawabin Ologunagba ya na cewa ana sayen fam a kan N100m ne domin a kaucewa saba dokar kamfe

Abuja - Jam’iyyar hamayya ta PDP ta zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da jagorantar ‘wawurar dukiyar al’umma’ domin a tunkari zabe mai zuwa.

Daily Trust ta bayyana cewa Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba ya zargi gwamnatin APC da tara kudin sata da sunan fam din takara.

A jawabin da ya fitar a ranar Talata, 10 ga watan Mayu 2022, Debo Ologunagba ya ce jam’iyyar hamayyar ta ga bukatar ankarar da mutane halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

A cewar kakakin na jam’iyyar PDP, kudin da ya kamata ayi wa al’ummar Najeriya aiki, kuma a biya ma’aikata albashi ne duk su ke tafiya aljihun takaran APC.

Saboda a wawuri kudin da ke cikin Baitul-mali ne APC ta tsaida fam din neman takarar shugaban kasa a kan Naira miliyan 100, a cewar jami’in jam’iyyar adawar.

Tribune ta ce PDP ta fito ta na ikirarin samun bayanan da suka tona yadda aka sace kudi daga ma’aikata da hukumomin gwamnati wajen yankan fam a APC.

APC ta saida fam a kan N100m
Yahaya Bello ya saye fam a APC Hoto: www.tori.ng
Asali: UGC

Ana sayen fam ga 'yan ci-ranin siyasa

Ologunagba ya ce kudin kasa sun fada hannun wasu da babu wanda ya san sana’arsu, wadanda suka fito su na cewa sun biyawa boyayyun 'yan siyasa kudin fam.

A cikin wadanda aka sayawa fam din nuna sha’awa da shiga takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, akwai wadanda ake ganin ba su da kima a siyasa.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Dole hukuma ta dauki mataki - PDP

A dalilin haka, PDP ta yi kira ga hukumar EFCC, Akanta-Janar da babban mai binciken kudi na kasa, su sa ido a wajen ganin yadda dukiyar gwamnati ke yawo.

Kakakin PDP ya ce ya kamata a lura da kyau domin a Baitul-malin kasa yayin da aka tunkari zabe. A cewarsa, babu abin da zai iya hana APC shan kasa a 2023.

“Kamar yadda doka ta ba ta damar fallasa rashin gaskiya, Majalisar tarayya ta nuna kishin kasa, ta fara binciken duk abubuwan da suke faruwa.”
“APC ta komawa hakan ne domin ta lura shugabanninta ba za su iya bada gudumuwa ba, saboda za su zaba dokar kudin da ake kashewa a kamfe.”

- Debo Ologunagba

Za ayi taron PDP NEC

A yau mu ka samu rahoto Majalisar kolin jam’iyyar PDP za ta yi zama na musamman a babban ofishinta da ke Abuja domin tattauna muhimman batutuwa.

A wannan zaman NEC na 97, za a amince da maganar yankin da za a ba takarar shugaban kasa. Shugabannin za kuma su tsaida inda za ayi zaben bada tuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel