'Yan siyasar Najeriya 10 da suka mallaki makudan kudi fiye da ragowar

'Yan siyasar Najeriya 10 da suka mallaki makudan kudi fiye da ragowar

Ba boyayyen abu bane cewar manyan 'yan siyasar Najeriya sun tara kazamin arziki daga mukamai daban-daban suka rike a gwamnati.

Wani nazari da bayanai da jaridar Forbes ta fitar a watan Satumba na shekarar nan da muke ciki, 2018, ya lissafa 'yan siyasar Najeriya 10 dake sahun gaba a tarin dukiya.

10. Ben Murray Bruce - Dalar Amurka miliyan$715m: Sanatan Najeriya daga jihar Bayelsa a karkashin jam'iyyar PDP, Ben Bruce, shine ya mallaki kamfanin Silverbird da ke da gidan talabijin da sinima.

Kafin ya zama sanata, Ben Bruce ya taba rike gidan talabijin na kasa (NTA) daga 1999 zuwa 2003.

9. Dino Melaye - Dalar Amurka miliyan $802m: Sanatan Najeriya daga jihar Kogi a karkashin jam'iyyar APC kafin daga baya ya canja sheka zuwa PDP.

Melaye ya mallaki asusun ajiyar kudi a kasar Amurka, duk da yin hakan ya saba da dokokin Najeriya.

8. Adamu Mu'azu - Dalar Amurka $895m: Tsohon gwamnan jihar Bauchi daga 1999 zuwa 2007, sannan tsohon shugaban jam'iyyar PDP daga 2014 zuwa 2015.

Kafin ya zama gwamna, Mu'azu kasance shugaban kwamitin gudanarwa na makarantar kimiyya da ke Idah daga 1984 zuwa 1986, shekarar da ya zama shugaban wani kamfanin gine-gine mai suna "Benue Construction Company" dake jihar Filato har zuwa shekarar 1997.

Mu'azu yana da aure da 'ya'ya 9.

7. Rotimi Amaechi - Dalar Amurka biliyan $1.3b: A ranar 27 ga watan Nuwamba, 2013, ne Rotimi Amaechi ya canja sheka daga PDP zuwa APC.

Kafin ya fita daga PDP, Amaechi ya kasance shugaban majalisar dokokin Ribas kafin daga bisani ya zama gwamnan jihar duk a jam'iyyar.

Amaechi na daga cikin 'yan siyasar Najeriya da hukumar tsaro ta FBI a kasar Amurka ta bayyana cewar sun ajiye kudi makudai a bankunan kasar. Rahotanni sun bayyana cewar Amaechi ya ajiye Dalar Amurka miliyan $757 a wani bankin kasar Amurka da ke Minnesota.

6. Ifeanyi Ubah - Dalar Amurka biliyan $1.7b: Hamshakin dan kasuwa ne a bangaren man fetur da sinadarin iskar gas kafin daga baya ya fadada harkokinsa zuwa gine-gine, sufuri da wasanni.

Ubah ya taba tsayawa takarar gwamnan jihar Anambra a karkashin jam'iyyar Labor Party, sai dai bai kaj ga nasara ba.

5. Atiku Abubakar - DalarAmurka biliyan $4b: Kafin ya zama mataimakin shugaban kasa a shekarar 1999, Atiku ya shafe tsawon shekaru 20 yana aiki da hukumar kwastam ta kasa.

Atiku ya mallaki wani kamfanin Intels da ke harkar man fetur tsakanin kasa da kasa, jami'ar AUN a Yola da ragowar wasu kamfanoni da masana'antu masu yawa.

4. Rochas Okorocha - Dalar Amurka biliyan $5bn: Tun kafin ya shiga harkokin siyasa, Rochas ya yi suna wajen aiyukan taimako da tallafawa masu karamin karfi a fadin Najeriya daga ribar da yake samu daga harkokinsa na kasuwanci.

A ranar 6 ga watan Mayu na shekarar 2011 ne aka fara zaben Rochas a matsayin gwamnan jihar Imo a karo na farko kafin ya kara lashe zabe a karo na biyu a shekarar 2015.

Kamar Rotimi Amaechi, Rochas na da kudin da adadinsu ya kai biliyan $1.45 a asusunsa na bankin kasar Amurka, JP Morgan, dake New York.

3. Bola Tinubu - dalar Amurka biliyan $32.7bn: Tsohon mamba a majalisar dattijai Najeriya daga yammacin jihar Legas karkashin jam'iyyar SDP a shekarar 1993, Tinubu ya zama gwamnan jihar Legas daga shekarar 1999 zuwa 2007.

2. Olusegun Obasanjo - Dalar Amurka biliyan $35bn: Tsohon shugaban kasa a mulkin soja daga shekarar 1976 zuwa 1979 kafin daga bisani ya zama shugaban kasa a tsarin dimokradiyya daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Obasanjo ya mallaki gona a Otta, jihar Ogun, mafi girma a nahiyar Afrika. Akwai ma'aikata fiye da 6,000 a gonar.

1. Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) - Dalar Amurka biliyan $50bn: Ya mulki Najeriya a mulkin soja daga shekarar 1983 zuwa 1993.

Ya rike mukamai masu yawa a hukumar sojin Najeriya kafin ya zama shugaban kasa.

A shekarar 1987 ne IBB ya kirkiri karin jihohi biyu: Akwa Ibom da Katsina.

Kazalika ya kirkiri karin wasu jihohin 9 da suka hada da: Abiya, Enugu, Delta, Jigawa, Kebbi, Osun, Kogi, Taraba da Yobe, a shekarar 1991.

Babangida ne shugaban kasar da ya dawo da hedkwatar Najeriya Abuja daga Legas a shekarar 1991.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel