Allah ya ji kanki: Dino Melaye ya yiwa APC ba'a bayan barkewar rikicin shugabanci a jam’iyyar

Allah ya ji kanki: Dino Melaye ya yiwa APC ba'a bayan barkewar rikicin shugabanci a jam’iyyar

  • A yanzu haka, rikicin shugabanci ya baibaye jam'iyyar APC gabannin babban taronta na kasa
  • Sanata Dino Melaye ya yi amfani da wannan damar wajen yi mata ba'a, inda ya ce an yi juyin mulki a jam'iyyar mai mulki
  • Ya kuma sanar a shafinsa na soshiyal midiya cewa APC ta mutu tare da yi mata addu'an samun rahama

Gabannin babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda za a yi a ranar 26 ga watan Maris, sabon rikicin shugabanci ya kunno kai a jam’iyyar mai mulki.

Hakan ya biyo bayan darewa kujerar Gwamna Mai Mala Buni da Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya yi a matsayin shugaban riko na jam’iyyar ta kasa, a ranar Litinin, 7 ga watan Maris.

Allah ya ji kanki: Dino Melaye ya yiwa APC ba'a bayan barkewar rikicin shugabanci a jam’iyyar
Allah ya ji kanki: Dino Melaye ya yiwa APC ba'a bayan barkewar rikicin shugabanci a jam’iyyar Hoto: dinomelaye
Asali: Instagram

Wannan ya sa Sanata Dino Melaye, tsohon dan majalisa da ya wakilci Kogi ta yamma a majalisar dattawa, yiwa jam’iyyar mai mulki ba’a.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Na dade ina rike da mukamin shugaban APC, gwamnan Neja

An yi juyin mulki a APC – Dino Melaye

Dino ya je shafinsa na Instagram inda ya yi wani rubutu kan rikicin na APC sannan ya ce an yi juyin mulki a jam’iyyar mai mulki.

Ya ce:

“Kwace ya kwace daga hannun wanda ya kwace…. yepaaaaa. Juyin mulki a APC.”

APC ta mutu, Allah ya ji kanta

Dan siyasar bai tsaya a nan ba, ya kuma wallafa cewa APC ta mutu tare da yi mata addu’an Allah ya ji kanta.

Ya rubuta a shafin nasa:

“RIP APC: 2014 - 2022. Shekaru 8. Kin tafi da wuri haka. Mai sanarwa – SDM”

Sabon shugaban APC ya dauki matakin farko na dunkule jam’iyya kafin Mala Buni ya dawo

A gefe guda, mun ji cewa a wani yunkuri na tabbatar da zamansa shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya, Abubakar Sani Bello, ya kira taron majalisar koli na NEC.

Kara karanta wannan

Sanusi II: Abu 1 da ya sa Jonathan da Ganduje suka tsige ni daga CBN da sarautar Kano

Jaridar This Day ta ce sabon shugaban kwamitin na CECPC, Gwamna Abubakar Sani Bello ya yi zama na farko da sauran ‘yan majalisarsa na rikon kwarya.

A wajen wannan zaman a majalisar koli watau NEC za a tabbatar da zaman Abubakar Sani Bello shugaban APC. Wannan rahoto ya zo a gidan talabijin Arise.

Asali: Legit.ng

Online view pixel