Kano: Mutane 4 Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata Bayan Ganduje Ya Rantsar Da Shugabannin APC

Kano: Mutane 4 Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata Bayan Ganduje Ya Rantsar Da Shugabannin APC

  • Wani tashin hankali ya afka tsakanin magoya bayan ‘yan takara biyu na gwamnan Jihar Kano yayin da ake tsaka da bikin rantsar da jami’an jam’iyyar APC
  • A ranar Asabar, gwamnan Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya rantsar da jami’ai na jam’iyyar a karamar hukumar Rano wanda ya tayar da kura
  • Sakamakon rikicin, mutane 4 sun rasa rayukansu yayin da wasu suka samu raunuka bayan magoya bayan ‘yan takarar gwamna, Murtala Garo da Kabiru Rurum suka yi batakashi

Kano - Rikici ya hautsine tsakanin ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar APC na zaben 2023 mai zuwa, Murtala Garo, kwamishinan harkokin kananun hukumomi da na Kabiru Rurum, dan majalisar wakilai na mazabar Rano, Kibiya da Bunkure.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya nada jami’an jam’iyyar APC a karamar hukumar Rano, wanda a dalilin shagalin mutane 4 suka rasa rayukansu sannan wasu da dama suka samu raunuka.

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

An gabatar da taron ne a filin wasan Rano inda aka raba ababen hawa ga sababbin jami’an jam’iyyar a mazabar Kano ta kudu, Premium Times ta ruwaito.

Kano: Mutane 4 Sun Rasa Rayukan Su, Da Dama Sun Jikkata Bayan Ganduje Ya Rantsar Da Shugabannin APC
Mutane 4 Sun Rasa Rayukan Su, Da Dama Sun Jikkata Bayan Ganduje Ya Rantsar Da Shugabannin APC a Kano. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

An yi nadin ne bayan watan da ya gabata kotu ta amince da shugabannin jam’iyyar da amintattun Ganduje suka zaba shekarar da ta wuce cikin jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga Garo har Rurum suna son maye gurbin Ganduje ne da zarar ya sauka inda ko wanne yake ta neman ganin APC ta tsayar da shi takara a 2023.

Mutane 4 sun rasa rayukan su

Daya daga cikin mamatan, Hamisu Abdullahi, wanda aka fi sani da Aga, mazaunin Kofar Gabas ne da ke Barkum a karamar hukumar Bunkure.

Kanin sa, Abba Abdullahi ya sanar da Premium Times cewa an birne gawar sa a ranar Asabar da dare, bayan ya mutu sakamakon sarar sa da aka yi yayin rikicin.

Kara karanta wannan

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

Ya ce mamacin mahauci ne, kuma ya dakata daga sana’ar sa bayan an kira shi ta salula inda aka gayyace shi taron siyasar da aka yi a Rano.

Ya rasu ya bar matarsa da yaronsa, kamar yadda majiyar ta kara.

Dayan wanda ya rasun, Dan-Mamadu Kaura dan asalin garin Garo ne da ke karamar hukumar Kabo, wanda ma’aikacin karamar hukuma ne.

Kaura bafulatani ne mai kiwon shanu wanda ke zama a wajen garin Garo. Bai dade da samun aikin shara ba a karamar hukumar Rimin Gado.

Majiyar ta shaida cewa yana cikin tawagar kwamishinan harkokin kananun hukumomi, Garo.

‘Yan daba ne suka afko filin ana tsaka da taron

Mazauna yankin sun bayyana yadda wasu ‘yan daba suka bayyana cikin filin wasan inda suka far wa abokan adawar su wadanda suka ji rauni har aka kai su asibiti.

Mazaunan sun bayyana yadda rikicin ya janyo tashin hankali ga mazauna yankin da kuma masu sana’a a kusa da asibitin da aka kai masu raunukan.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Kasa ta rufta da mutum 5 a garin taya abokinsu hakar kasar ginin aurensa

Wata majiya daga asibiti ta sanar da Premium Times yadda aka kai akalla mutane 6 asibitin kuma mutum daya ya rasu.

Wani mazaunin garin Rano, Ibrahim Yusuf ya ce sauran mutane 2 da aka halaka a wurin ba ‘yan Rano bane, sai dai daga Kano suka zo. Yusuf ya ce ‘yan sanda sun dauke gawawwakin su bayan aukuwar lamarin.

Kakakin gwamna Ganduje, Abubakar Ibrahim ya shaida yadda Ganduje ya nada jami’ai daga mazabu 16.

Sannan ya ce gwamnan ya bayar da ababen hawa ga sabbin jami’an. Kuma manyan mutane kamar shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado-Doguwa da dan majalisa mai wakiltar mazabar Rano, Kibiya da Bunkure, Rurum suka samu halartar taron.

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Haruna Kiyawa, ya ce zai nemi wakilin Premium Times, amma har lokacin rubuta rahoton nan bai yi hakan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel