Da duminsa: Nan da yan sa'o'i Buhari zai rattafa hannu kan sabuwar dokar zabe, Femi Adesina

Da duminsa: Nan da yan sa'o'i Buhari zai rattafa hannu kan sabuwar dokar zabe, Femi Adesina

  • Mai magana da yawun da shugaban kasa ya bayyana lokacin Buhari zai rattafa hannu kan dokar zabe
  • Kungiyoyin raya demokradiyya da fafutuka sun yi barazanar yin zanga-zanga idan Buhari ba sanya hannu
  • Da farko Buhari ya yi watsi da dokar zaben saboda majalisa na kokarin wajabta zaben yar tinke

Birnin Abuja - Nan da yan awanni Shugaba Muhammadu Buhari zai rattafa hannu kan dokar zaben da aka yiwa gyaran fuska yayinda ake shirin shiga zaben 2023.

Mai magana da yawun Shugaban kasa, Mr Femi Adesina, ya bayyana hakan ranar Talata yayin hira a shirin Sunrise Daily na tashar ChannelsTV.

Yace:

"Zai rattafa hannu kan dokar nan ba da dadewa ba. La'alla yau, ko gobe, ko wani lokaci, a watan nan."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamnonin APC sun shiga ganawar gaggawa da Shugaba Buhari

"Nan da awanni, ba kwanaki ba. Mai yiwuwa awanni 24, ko 48, amma ba ranaku ko kwanaki ba."

Femi Adesina
Da duminsa: Nan da yan sa'o'i Buhari zai rattafa hannu kan sabuwar dokar zabe, Femi Adesina Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Ina goyon bayan Buhari kan kin sanya hannu a dokar zabe, Sanata Adamu

Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, cewa ya yi farin ciki da ganin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai sanya hannu a gyararren dokar zabe ba.

Adamu ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya a Keffi cewa Majalisar dokokin bata da hurumin aiwatar da wani kudiri da zai yanke yadda jami’iyyu za su zabi yan takararsu.

Adamu ya ce ba bakon abu ne kuma rashin adalci ne a zo da wani doka da zai takaita yadda jam’iyyu za su gudanar da zabensu.

Yace yana goyon bayan shugaban kasa a kan kin saka hannu a kudirin.

Yac ya kamata mu yi godiya cewa kin saka hannun da Buhari yayi yana da amfani sosai. Shi mutum ne mai alkibla; mai zurfin tunani da tsare-tsare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel