Fashola: Buhari ya yi wa Gwamnatin Amurka fintinkau a ɓangaren yin ayyukan more rayuwa

Fashola: Buhari ya yi wa Gwamnatin Amurka fintinkau a ɓangaren yin ayyukan more rayuwa

  • Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya ce gwamnatin APC ta samu nasarori masu yawa fiye da gwamnatin Amurka dangane da ababen more rayuwa
  • Fashola ya yi wannan furucin ne yayin wani taro na wayar da kan jama’a a kan nasarorin jam’iyyar APC cikin shekaru 7 da suka gabata wanda aka yi a Kano ranar Alhamis
  • Kamar yadda ministan yace, daga 2015 zuwa watan Disamban 2021, gwamnati ta kammala tituna masu tsawon kilomita 941 a cikin jihohi da yankuna daban-daban na kasar nan

Jihar Kano - Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya ce gwamnatin jam’iyyar APC ta samu nasarori fiye da ta Amurka a bangaren yin ayyukan more rayuwa, Daily Trust ta ruwaito.

Mr Fashola ya yi wannan furucin ne ranar Alhamis a Kano yayin wani taron tattaunawa na jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Fashola: Buhari ya yi wa Gwamnatin Amurka fintinkau a ɓangaren samar da kayayyakin more rayuwa
Buhari ya yi wa Gwamnatin Amurka fintinkau a ɓangaren samar da kayayyakin more rayuwa, Fashola. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

An yi taron ne musamman don wayar da kan jama’a akan nasarorin da jam’iyyar ta samu cikin shekaru 7 da suka shude.

Daga 2015 zuwa Disamban 2021 an kammala titina masu tsawon kilomita 941

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Ministan ya ce:

“Ina mai tabbatar muku mulkin APC bisa jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu nasarori masu yawa fiye da na gwamnatin Amurka idan a bangaren kayan more rayuwa ne.
“Zuwa Disamban 2021, mun kammala gina hanyoyi masu tsawon kilomita 941 a yankuna daban-daban na kasar nan.
“A nan Kano kuwa akwai ayyukan titina 21 a ciki da kuma garuruwan da suka sadu da jihar.”

A cewarsa a gwamnatin baya ana sata ba tare da yin ayyukan a zo a gani ba

Kara karanta wannan

Matsayin Da Ake Ciki Akan Sulhu da yan tsagin Gwamna Ganduje, Malam Ibrahim Shekarau

Ya ce kafin zuwan mulkin APC, da kyar mutum ya ga gwamnatin tarayya ta yi titi mai tsawon kilomita 50.

Saboda haka ne ya ce an ga canji mai kyau wanda gwamnatin ta yi wa ‘yan Najeriya alkawari a 2015. Wanda a gwamnatin baya sai sata babu ayyuka.

A cewar Fashola, yanzu haka akwai ayyuka 850 na hanyoyi wadanda ma’aikatar sa take kulawa da su ciki har da gadoji tare da gidaje a jihohi 34 da ke kasar nan.

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin kakaba Ministan Buhari ya yi takarar Gwamna yake barka APC a Kebbi

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel