Shugabancin APC: Gwamnan Nasarawa da manyan masu ruwa da tsaki a jihar sun bayyana zabinsu

Shugabancin APC: Gwamnan Nasarawa da manyan masu ruwa da tsaki a jihar sun bayyana zabinsu

  • Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule da manyan masu ruwa da tsaki na APC a jihar sun lamuncewa Tanko Al-Makura domin ya zama shugaban jam'iyyar na kasa
  • Sule ya ce jihar Nasarawa ta cancanci samar da shugaban jam'iyyar mai mulki na kasa kuma lallai za su tabbatar da nasarar sanata Almakura a babban taro mai zuwa
  • Ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 25 ga watan Janairu, a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da ya gudana a Lafia

Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule da manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Nasarawa sun marawa tsohon gwamnan jihar, Sanata Umaru Al-Makura, domin ya haye kujerar kujerar shugaban jam'iyyar na kasa.

Da yake magana a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da ya gudana a Lafia a ranar Talata, 25 ga watan Janairu, Gwamna Sule ya ce sun lamuncewa Al-Makura ne domin ganin ya samu cikakken goyon baya da nasara a babban taron jam'iyyar mai zuwa, Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Magance tsaro: Tinubu ya bada tallafin miliyoyin Nairori ga jihar Neja

Za a dai gudanar da taron jam'iyyar ne a ranar 26 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Shugabancin APC: Gwamnan Nasarawa da manyan masu ruwa da tsaki sun lamuncewa Al-Makura
Shugabancin APC: Gwamnan Nasarawa da manyan masu ruwa da tsaki sun lamuncewa Al-Makura Hoto: The Sun
Asali: UGC

Gwamnan wanda ya bukaci yan asalin Nasarawa da kada su damu da rashin wasu manya a wajen taron ya ce labari mai dadi shine cewa jihar Nasarawa na da dan takara daya ne da ke neman kujerar shugabancin jam'iyyar, Vanguard ta rahoto.

Sule ya ce:

"Ina matukar farin ciki a yau saboda ni na fara wannan kamfen don jihar Nasarawa saboda na yarda cewa mun cancanci a bamu matsayin shugaban APC na kasa.
"Dukkanin jam'iyyun siyasar da suka hade don kafa APC sun samar da shugaban jam'iyya na kasa illa wannan jam'iyya kuma Tanko Al-Makura shine gwamna guda daya tilo a jam'iyyar a wancan lokacin.
"Zuwa yanzu, babu wani a jihar da ya fito fili ya ce yana son zama shugaban APC na kasa illa Al-Makura kuma za mu bashi cikakken goyon bayan da yake bukata don yin nasara."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fitar da jadawalin abubuwan da za su faru nan da gangaminta na kasa

Gwamnan ya roki shugabannin APC a matakin tarayya da fadin jihohi 36 na kasar da su marawa Al-Makura baya domin ya zama shugaban jam'iyyar na kasa don tabbatar da ci gaba da nasarar jam'iyyar.

Shugaban kasa a 2023: Tinubu na ci gaba da zawarci, ya ziyarci babban jigo na APC

A wani labarin, babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa, Sanata Sani Musa (APC Neja).

Ziyarar Tinubu na zuwa ne kwanaki uku bayan Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya lamunce ma kudirinsa na neman takarar shugaban kasa.

Sanata Musa na daya daga cikin manyan yan takara da ke neman takarar kujerar shugabancin jam'iyyar APC na kasa a babban taron jam'iyyar mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel