Wata Sabuwa: Kakakin Jam'iyyar APC ya yi murabus daga kan mukaminsa, zai koma PDP

Wata Sabuwa: Kakakin Jam'iyyar APC ya yi murabus daga kan mukaminsa, zai koma PDP

  • Kakakin jam'iyyar APC reshen jihar Delta, Sylvester Imonina, ya mika takardar murabus daga kan mukaminsa ga shugaban APC
  • Mista Imonina, yace ya ɗauki wannan matakin ne saboda yanayin yadda ake tafiyar da harkokin APC a jihar
  • Wata majiya mai karfi ta tabbatar da cewa tsohon kakakin APC ya kammala shirin komawa jam'iyyar PDP

Delta - Kakakin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya reshen jihar Delta, Mista Sylvester Imonina, ya yi murabus daga mukaminsa, kuma ya fice daga jam'iyya.

Punch ta rahoto cewa Imonina ya miƙa takardar murabus ɗinsa, mai ɗauke da kwanan watan 18 ga watan Janairu, 2022, ga shugaban APC na jihar.

Tsohon kakakin ya bayyana cewa ya jefar da kwallon mangwaro domin ya huta da ƙuda saboda, "Wasu dalilai da suka sha ƙarfinsa."

APC da PDP
Wata Sabuwa: Kakakin Jam'iyyar APC ya yi murabus daga kan mukaminsa, zai koma PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A takaradar murabus ɗin da manema labarai suka ci karo da ita ranar Laraba. Mista Imonina, ya ce:

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duba da halin da APC reshen jihar Delta ta tsinci kanta, Ni Ogheneluemu Sylvester Imonina, na yi murabus daga kasancewa ta mamba da kuma mukamin mukaddashin kakaki."

Kalaman da ya yi wa APC

Mista Imonina ya gode wa shugabancin APC a matakin karamar hukuma da jiha bisa duba cancantarsa har suka amince masa ya yi aiki a wannan matsayin.

Takardar murabus ɗin kakakin ta biyo ta hannun shugaban APC na gundumar Isoko North ta II, ya gode wa baki ɗaya shugabanni bisa ba shi damar kasancewa cikin waɗan da suka gina jam'iyya.

Rahoto ya nuna cewa ya ɗauki wannna matakin ne sabida zargin cewa mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Omo-Agege, ya yi babakere kan tafiyar da jam'iyyar baki ɗaya.

Wace jam'iyya zai koma?

Da yake tabbatar da murabus ɗinsa ga wakilan mu, tsohon kakakin ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mutane sun shiga daji sun kwato Sarkin su da yan bindiga suka sace a Filato

"Ɗan uwa, abin da kuka gani gaskiya ne, na aje mukamina a kwamitin gudanarwa (SWC), sabida yanayin tafiyar da harkokin jam'iyya."
"A halin yanzun ban yanke hukunci kan jam'iyyar da zan koma ba, ina bukatar nazari da kaina kafin nan."

Sai dai, wata majiya mai karfi, ta shaida mana cewa Mista Imonina, ya kammala shirin komawa PDP a wani babban taro da za'a gudanar ranar Asabar a Asaba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma mai kama da wannan Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki

Mista Famuyibo, yace alamu sun nuna wanda gwamna ke so shi jam'iyyar APC zata baiwa tikitin takarar gwamnan Ekiti a zaben dake tafe 2022

A cewarsa, babu dalilin da zai sa ya cigaba da zama a APC duba da bukata da burin al'umma a akan sa na ya fito takarar gwamnan Ekiti.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani kan kyautar da Tinubu ya bayar na N50n ga 'yan Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel